Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, ta kama ƙaurayen da suka addabi jama’a da satar wayoyi

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, ta sanar da kama wasu mashahuran mutane 2 da aka fi sani da Ƙauraye, waɗanda suka shiga wani shago tare da sace wayoyin hannu guda 48.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Gambo Isah ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Katsina.

Ya ce an kama waɗanda ake zargin Abubakar Haruna mai shekaru 23 da Ibrahim Sani mai shekaru 22 a Katsina a ranar Laraba bisa samun sahihan bayanan sirri.

KU KUMA KARANTA: Wuta ta kama wani mutum lokacin da yake tsaka da satar waya a taransfoma

Mista Isa ya yi zargin cewa waɗanda ake zargin sun haɗa baki ne da wani Tayi, wanda a halin yanzu ya kai kuma suka yi fashin kantin sayar da wayar salula da ke Tsohuwar Tasha, Katsina, tare da sace wayoyin hannu guda 48 da aka samu a hannunsu.

Ya yi iƙirarin cewa waɗanda ake zargin sun amsa laifinsu, kuma ya ce suna so ne su sayar da wayoyin da aka sace a wata ƙasa da ke maƙwabtaka da su.

Kakakin rundunar ’yan sandan ya ce, za a gano mutanen biyu da sauran waɗanda ake zargin, tare da kama su da kuma gurfanar da su a gaban ƙuliya.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *