Rashin tsaro: Gwamnan Yobe ya gana da babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya

0
93
Rashin tsaro: Gwamnan Yobe ya gana da babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya

Rashin tsaro: Gwamnan Yobe ya gana da babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya

Daga Ibraheem El-Tafseer

Gwamnan Jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni CON, ya gana da babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, kan taɓarɓarewar tsaro a jihar.

Buni ya bayyana damuwarsa kan sabon salon ta’addanci da ‘yan ta’adda suka yi a jihar waɗanda suka kai hari haɗe da kashe-kashe da sace dukiyoyi a wurare a mabambanta da ke kan iyakokin ƙasar.

A wata sanarwa da Mamman Mohammed, babban Daraktan yaɗa labarai na Gwamnan Yobe ya sanya wa hannu, ya ce, “ an samu ci gaba sosai a fannin tsaro a faɗin jihar, in ban da yadda ‘yan ta’adda suka kawo a makon nan, kuma hare-hare ya fi shafar al’ummomin da ke kan iyaka.

“Abin takaicin shi ne, kwanaki uku da suka gabata, mun samu labarin harin da ‘yan ta’adda suka kai a ƙauyen Mafa da ke kan iyaka da jihar Borno, da kuma ‘yan kwanakin baya, a garin Geidam da ke kan iyaka da jamhuriyar Nijar, inda muka rasa rayuka da dama.

“Na tattauna sosai da jami’an CDS domin samun mafita mai ɗorewa kan wannan kutse da hare-haren da ake kaiwa al’ummomin kan iyaka.

KU KUMA KARANTA: Yadda Boko Haram a Yobe suka kashe mutane da dama

“Na ji daɗin martanin da ya bayar, da kuma sabbin dabarun da ya ba da tabbacin ɗaukarwa don duba barazanar da ‘yan ta’adda ke yi don kare rayuka da dukiyoyin jama’armu,” in ji Gwamna Buni.

Gwamnan ya ba da tabbacin goyon bayan gwamnatinsa ga dukkan hukumomin tsaro a jihar domin yaƙi da miyagun laifuka yadda ya kamata, da kuma ƙarfafa zaman lafiya da tsaro a faɗin jihar Yobe.

Janar Musa ya ce sojojin za su tura ƙarin jami’ai da sabbin dabaru don kawo ƙarshen motsi da hare-haren da ‘yan ta’adda ke kaiwa a yankunan da aka gano.

Ya ba da tabbacin inganta haɗin gwiwa tsakanin sojoji da al’ummomi domin haɗa kai da samun nasarar murƙushe ta’addanci a Najeriya da sauran nau’in laifuka a faɗin ƙasar baki ɗaya.

Leave a Reply