Za mu kammala aikin layin dogo daga Ibadan-Abuja-Kaduna-Kano ba da jimawa ba – Gwamnatin tarayya

0
19
Za mu kammala aikin layin dogo daga Ibadan-Abuja-Kaduna-Kano ba da jimawa ba - Gwamnatin tarayya

Za mu kammala aikin layin dogo daga Ibadan-Abuja-Kaduna-Kano ba da jimawa ba – Gwamnatin tarayya

Daga Idris Umar, Zariya

Gwamnatin tarayya ta ce za ta kammala aikin titin jirgin ƙasa daga Ibadan-Abuja-Kaduna-Kano nan ba da jimawa ba.

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da tabbacin za a kammala aikin titin jirgin ƙasan wanda ya tashi daga Ibadan zuwa Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano don inganta harkar sufuri a Najeriya da yammacin ƙasashen Afirka baki ɗaya.

Mai magana da yawun Shugaba Tinubu, Ajuri Ngelale ne, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, ya ce, Tinubu ya bayyana haka ne yayin wata ziyara da ya kai Hedikwatar kamfanin gina layin dogo na ƙasar Sin (CRCC) a birnin Beijing.

KU KUMA KARANTA: Najeriya ta samu tallafin dala biliyan 1.3 Don ƙarasa hanyar jirgin ƙasa daga Kano zuwa Nijar

Shugaban ya amince da rawar da kamfanin ke takawa a matsayin amintaccen abokin hulɗar Gwamnatin Tarayya a cikin shirin samar da ababen more rayuwa ga ‘yan Najeriya, ya kuma yaba da ayyukan da yake yi na gina layin dogo a Najeriya.

Yace yana da matuƙar muhimmanci ya baiwa al’ummar Najeriya tabbacin cewa a duk faɗin ƙasar, za a kammala aikin layin dogo daga Ibadan-Abuja-Kaduna-Kano, da kuma inganta sufuri a Najeriya da yammacin Afrika baki ɗaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here