PDP-NYA Kaduna, Ta Ƙaddamar Da Shirin Wayar Da Kan Al’umma Daga Matakin Kasa

1
874

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

KUNGIYAR matasan Jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP-NYA) reshen Jihar Kaduna, ta kaddamar da shirinta na wayar da kan al’umma daga matakin kasa ta hanyar Kafafen sada zumunta da Yada Labarai wato “Grassroots Mobilisation and Media Advocacy Programme” domin lalubo hanyoyin da za ta iya kwato mulki a zaben shekara ta 2023 mai zuwa.

A yayin taron wanda ya gudana a Arewa House Kaduna a ranar Asabar din da ta gabata, mai taken ” Kalubale da Gudummawar Matasa Ga Ci gaban Jam’iyyar PDP a Jihar Kaduna, Kungiyar PDP-NYA ta ce lokaci ya yi da za su kwato hakkinsu da mukamansu a Jihar Kaduna.

Da yake jawabi a wajen taron, shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Ahmed Muhammad Makarfi, ya bayyana cewa Jam’iyyar ta taka muhimmiyar rawa wajen inganta tare da shigar da matasa cikin harkokin Jam’iyyar a kasar nan, inda ya ce yanzu ya rage su yi amfani da damar su.

Sanatan da ya samu wakilcin tsohon kwamishinan wasanni na Jihar Kaduna, Honorabul Shehu Adamu, ya kara da cewa matasan suna da babban aiki na hada kai domin samar da hadin kai a fadin kasar nan domin neman abin da suke so, ya kuma bukace su da yin tanadin katin zabe da zasu kada kuri’unsu lokacin zaben 2023.

Ya ce, “Ba ni da shakka, da irin yawan Matasan da na gani a yau sun taru a wajen nan, hakan na nuni da cewa a shirye suke domin yin aikin da ya dace kuma Jam’iyyar PDP ba kawai Jihar Kaduna zata kwace ba, har ma da Najeriya baki daya.”

Sanata Makarfi, ya yi kira ga daukacin Matasan kasar nan, da cewa duk abin da suke son zama a cikin harkar siyasa ta hanyar tsayawa takara, su tabbata sun tanadi katin zabensu da zummar kada kuri’arsu bisa ra’ayinsu ga wanda suka ga dama.

A nasa jawabin, shugaban Kungiyar PDP-NYA na Kaduna, Kwamared Ahmad Ashir, ya bayyana cewa kungiyar ta PDP-NYA, ta dauki aniyyar ganin cewa jam’iyyar PDP ta kwato mukamanta a kasar nan ta hanyar shirin nan na wayar da kan al’umma wanda suka yiwa taken ‘Grassroots Mobilisation And Media Advocacy Program’.

Ya ce, “Abin da ya sa mu shirya wannan taron shi ne ganin cewa an yi watsi da matasa a harkokin siyasa, don haka abin da muke yi a halin yanzu shi ne hada kan matasa da mata da su rungumi sana’ar siyasa.

Kwamared Ashir, ya kara da cewa kungiyar ta dauki alhakin wayar da kan al’umma a kafafen sadarwa na zamani da na kafafen yada labarai na yau da kullum don kaucewa dabi’ar siyan kuri’u da siyar da yan kai wanda daga karshe za su yi nadama a tsawon rayuwarsu.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here