Ododo ya zama ɗan takarar gwamna na jam’iyar APC a Kogi

0
1439

Ahmed Ododo ya zama ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Kogi. A cewar Patrick Obahiagha, sakataren kwamitin zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC na Kogi, Ododo ya samu ƙuri’u 78, 704 inda ya doke sauran ‘yan takara shida.

Mista Obahiagha wanda ya bayyana sakamakon zaɓen fidda gwani na gwamna a ranar Juma’a a Lokoja, ya ce Salami Momodu ya samu ƙuri’u 1,506; Abubakar Yahaya-Ashemogu 1,159 da; Shaaibu Abubakar-Audu, 763. Ya ƙara da cewa Stephen Ocheni ya samu ƙuri’u 552, yayin da Sanusi Ohiere da Smart Adeyemi suka samu ƙuri’u 424 da 311.

Mista Obahiagha ya ce daga cikin masu kaɗa ƙuri’a 93,729, 83,419 da aka amince da su, sun zaɓi ‘yan takarar da suke so.

KU KUMA KARANTA: Bomai ya lashe zaɓen Sanatan Yobe ta kudu

“Ododo, bayan da ya samu rinjayen ƙuri’un da aka kaɗa a zaɓen fidda gwani da aka gudanar a ranar 14 ga Afrilu, 2023, a Kogi, an bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC a 2023.

“An dawo da Ahmed Usman-Ododo a matsayin zaɓaɓɓen ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaɓen gwamna na Nuwamba 2023,” in ji shi.

Mista Obahiagha ya taya shugabannin jam’iyyar da membobin jam’iyyar murnar zaɓen fidda gwanin da aka gudanar cikin lumana. Sakataren kwamatin ya kuma miƙa godiyarsa ga Gwamna Yahaya Bello, kan yadda tsarin dimokraɗiyya ya samu.

Leave a Reply