NYSC ta yi tattakin bikin cika shekaru 50 da kafuwa a Yobe

2
332

A ci gaba da gudanar da bukukuwan cika shekaru 50 da kafa hukumar yi wa ƙasa hidima ta ƙasa (NYSC) da ta fara gudanar da tattaki na haɗin kai a faɗin ƙasar baki ɗaya domin fara jerin abubuwan da za su ɗauki tsawon mako guda.

A jihar Yobe, shugabar NYSC ta jihar (co’ordinator), Hajiya Hafsat Yerima ta jagoranci ɗaruruwan jami’an hukumar da jami’an tsaro a wani tattaki a wasu manyan titunan birnin Damaturu, babban birnin jihar Yobe.

Sun yi tattakin tare da ‘yan yiwa ƙasar hidima ɗauke da tutoci da alluna masu ɗauke da rubuce-rubuce daban-daban da ke nuna irin gagarumin ci gaban da aka samu a cikin shekaru hamsin da kafuwa.

Tun da farko kafin a fara tattakin, kodinetan jihar ta yi jawabi inda ta bayyana cewa; Hukumar NYSC na bikin cika shekaru 50 na hidimar sadaukar da kai ga bil’adama da sadaukarwa ga gina ƙasa da kuma ci gaban dukkan ɓangarorin ƙasa.

KU KUMA KARANTA: Hukumar NYSC ta damu da rashin kyawun yanayin sansanin a jihar Neja

Ko’odinetan ta godewa ɗaiɗaikun jama’a da ƙungiyoyi da gwamnatoci da masu ruwa da tsaki a kan yadda suka ba shirin NYSC goyon baya a tsawon shekaru.

Ta umurci membobin na ‘yan yiwa ƙasa hidima da su ci gaba da kasancewa jakadu nagari na wannan tsari a duk ayyukansu.

Babban abin da ya fi ɗaukar hankali shi ne lokacin da wasu jama’a suka shiga jerin gwano domin nuna godiya da kyawawan ayyukan da shirin ke yi.

2 COMMENTS

Leave a Reply