Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.
KWAMISHINAN ma’aikatar kula da kananan hukumomi na Jihar Zamfara Alhaji Abubakar Dambo, ya bayyana Jihar a matsayin wadda ta tserewa tsara a kan batun ma’adinai a duk fadin tarayyar Najeriya.
Kwamishinan wanda ya wakilci Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Dokta Bello Matawalle, ya ce babban abin da Jihar kawai a halin yanzu ke bukata shi ne addu’ar kara samun ingantaccen zaman lafiya ta yadda za a ci gaba da samun walwala da zaman lafiya.
“Akwai muhimman tsare tsaren da Jihar ke da su ta fuskar samar da ingantaccen tsarin maraba da duk mai son zuba jari a Jihar, kasancewar Jihar mai dimbin ma’adinan karkashin kasa da za a iya kafa masana’antun da za su amfani al’umma”.
Kwamishinan ya ci gaba da cewa muna da tsarin yin maraba da kowa domin zuba jarinsa ta fuskoki da dama a Jihar, wanda hakan ya sa Gwamnatin Jihar Zamfara tare da yin tsarin hadin Gwiwa ta samar da katafaren otal a cikin garin Gusau wanda idan an kammala komai zai taimaka wajen kara bunkasa tattalin arzikin mutanen Jihar Zamfara, kuma Jihar na kan kokarin ginin babban filin Jirgin sama domin jigilar kaya a kan kudi naira biliyan 15 wanda ba karamin ci gaba za a samu a Jihar ba”.
“Jihar Zamfara na yin takama ne da aikin Noma kasancewar babu wata karamar hukumar da babu ma’adinai ko kayan amfanin Gona.
Kwamishinan ma’aikatar kananan hukumomin ta Jiha ya kara da yin kira ga dukkan yan kasuwa da kamfanoni a fadin duniya da su zo Jihar Zamfara domin zuba jari.