Nishaɗin wasan ‘yar gala-gala da ‘yan mata ke yi

0
186

Wasan gargajiya ne da ya shahara a ƙasar Hausa wadda galibi yara ne musamman ‘yan mata ke yin sa.

Ana yin wasan tsakanin mutane biyu ko fiye ta hanyar zana layin murabba’i a ƙasa. A lokacin da ake wasan ana sa ran ɗan wasa ya jefi wani ɗan dutse kaɗan (wadda aka fi sani da ƙoduwa a ƙasar Hausa) a cikin wani layi na musamman na murabba’i sannan ya yi tsalle a kan sauran filayen ta hanyar tsallake filin da dutsen. Dole ne ɗan wasa ya yi haka kan duk murabba’i don cin nasarar kai wa matakin gida.

KU KUMA KARANTA: Amfanin rumbu wurin ajiye kayan aikin gona

‘Yar Gala-Gala wasa ne da ke taimaka wa ‘yan mata yin nazari da tunani, tare da inganta zamantakewa tsakanin yara a cikin wata al’umma. Haka nan, ya na samar da nishaɗi a cikin zukatan tare da inganta haɗin kai da ƙaunar juna.

Leave a Reply