Nijar ta ɓullo da wasu matakan inganta rayuwar marasa lafiya kyauta

0
78
Nijar ta ɓullo da wasu matakan inganta rayuwar marasa lafiya kyauta

Nijar ta ɓullo da wasu matakan inganta rayuwar marasa lafiya kyauta

Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun ɗauki matakin sassauta yawan kuɗaɗen da marasa lafiya ke biya a asibitocin gwamnati da kashi 50% yayin da kuma za a fara karɓar haihuwa da wankin ƙoda kyauta a ci gaba da ɓullo da matakan inganta rayuwar talakawan ƙasar.

A taron majalissar ministoci na yammacin ranar Alhamis ne aka ba da sanarwar yanke shawarar ɓullo da matakin na rage kashi 50% na kuɗaɗen da marasa lafiya ke biya a baya a asibitocin gwamnati.

Matakin ya shafi kwantar da marasa lafiya a asibiti, ganin likitoci da gwaje waje da bincike na na’urar radion xray da dai sauransu.

Haka kuma hukumomin a karshen wannan zama sun yanke shawarar shimfida tsarin karbar haifuwa kyauta a irin wadanan asibitoci da zummar sassauta wahalhalun talakkawan kasar musamman na yankunan karkara, abin da shugabar kungiyar kare hakkin mata da yara SOS FEVF Madame Ahmed Mariama Moussa ta yaba da wannan yunkuri.

KU KUMA KARANTA:Libya ta kora ‘yan Najeriya da Mali 463 Zuwa Nijar

A baya masu fama da cutar koda kan biya jaka 150 na cfa (150000 fcfa) don ci gaba da samun wankin koda har illa masha Allahu to amma a bisa la’akari da yadda biyan irin wadannan kudade ke zama jidali ga marassa lafiya ya sa gwamnatin yanke shawarar fara wannan aiki kyauta abin da Nayoussa Djimrao jigo a kungiyar MPCR ya bayyana a matsayin babban alheri.

Gamayyar kungiyoyin kare hakkin jama’a a fannin kiwon lafiya ta ROASSIN wace ta nuna farin ciki kan wannan mataki ta dai gargadi hukumomi game da bukatar zuba ido akan wannan sabon tsari ta yadda jama’a za su mori abinda aka yi domin ta bisa la’akari da yadda a shekarun baya shirin bada magani kyauta ga yara ‘yan kasa da shekaru 5 ya sha ruwa.

Daga ranar 1 ga watan Satumban 2024 ne za a fara zartar da wannan matakai a asibitocin gwamnati manya da kanana.

Leave a Reply