Mahara sun hallaka mutane 8 a jihar Neja

0
62
Mahara sun hallaka mutane 8 a jihar Neja

Mahara sun hallaka mutane 8 a jihar Neja

Wasu mahara da ake kyautata zaton mayaƙan Boko Haram ne sun hallaka mutum 8 akasarinsu matasa a jihar Nejan Najeriya.

Bayanai daga yankin Unguwar Mai goro kusa da Alawa a ƙaramar Hukumar shiroro na nuna cewa ‘yan bindigar sun auka wa mutanen ne a daidai lokacin da suke aikin haƙar ma’adanai a wannan wuri.

Wani da ya tsallake rijiya da baya da ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce, kuma ba ya ga waɗannan mutane 8 da aka ga gawarwakin wasu da dama sun faɗa wani ruwan kogi da ke kusa da wannan wuri kuma har ya zuwa lokacin da muke magana dashi ba a san yawan waɗanda suka faɗa ruwan kiginba.

Shugaban kamar hukumar ta shiroro Hon. Aƙilu kuta ya tabbatar da faruwar lamarin yanda yace suna cikin yanayi na tashin hankali.

KU KUMA KARANTA:Mahara a Benuwe sun kashe mutum 18 da sace magidanci da ’ya’yansa

Ita ma dai Gwamnatin jihar Neja ta fitar da wata sanarwa dake nuna takaicinta akan wannan ta’addanci.

Sanarwar mai ɗauke da sanya hannun sakataren labaran Gwamna umar Bago Malam Ibrahim Bolagi tayi Allah wadai da harin dake zama na keta tare da bayyana cewa Gwamnati na kokari sosai wajan daukar matakan shawo kan matsalar rashin tsaro da ya Addabi jihar.

Har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto dai babu wani karin haske daga rundunar yansanda ta jihar Nejan akan wannan hari domin kuwa kokarin samun kakakin yansandan wasiu Abiodun ta wayan salula yaci tura.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here