Netanyahu ya yi watsi da ƙiraye-ƙirayen tsagaita wuta

0
142

Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya yi watsi da ƙiraye-ƙirayen tsagaita wuta a yaƙi da Hamas.

Da yake magana a wani jawabi da aka watsa a gidan talabijin, Netanyahu ya ce ba zai amince da yunƙurin ba har sai Hamas ta saki ƴan ƙasar da tayi garkuwa da su a harin da ta kai ranar 7 ga watan Oktoba.

Yana jawabi ne jim kaɗan bayan Sakataren harkokin tsaron Amurka Antony Blinken ya ƙara yin ƙira na tsagaita wuta na wucin gadi don bai wa ƙarin kayan agaji damar shiga Gaza.

Blinken ya kuma ce hakan zai samar da yanayin muhalli mai kyau ta yadda za a saki waɗanda aka yi garkuwa da su.

Sai dai Netanyahu ya ce: “Isra’ila ta ki amincewa da buƙatar tsagaita wuta na wucin gadi ba tare da saka batun sako waɗanda aka yi garkuwa da su ba.”

Leave a Reply