Najeriya ta kwaso ‘yan ƙasarta 542 da suka maƙale a Dubai

0
638

Gwamnatin Najeriya ta kwashe ‘yan kasar kimanin 542 da suka makale a kasar hadaddiyar Daular Larabawa. A wani saƙo ta Hukumar da ke kula da lamurran ‘yan Najeriya mazauna ƙasashen waje ta wallafa a shafinta na Tuwita, ta ce da misalin karfe 4:29 na asubahin yau ne jirgin da ya kwaso mutanen ya sauka a filin jirgin saman Abuja babban birnin ƙasar.

Wannan na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan da hukumar shige da fice ta ƙasar Hadaɗɗiyar Daular Larabawa ta bayyana dakatar da bai wa ‘yan Najeriya biza, saboda wasu matsaloli da suka shafi diplomasiyya tsakanin ƙasashen biyu.

Rahotonni sun ambato gwamnatin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa na cewa duka waɗanda suka cika takardun neman biza za a mayar musu da takardunsu ba tare da samun amincewa ba.

Ta kuma ce ”ƙin amincewar ya shafi kowanne ɗan Najeriya, dan haka babu wanda za a ba shi biza a halin yanzu”.

A baya-bayan nan dai dangantaka na ƙara yin tsami tsakanin ƙasashen biyu, inda a watan da ya gabata ƙasar ta UAE ta daina bayar da bizar yawon buɗe ido ga ‘yan ƙasa da shekara 40, lamarin da ya shafi ‘yan Najeriya da na wasu ƙasashen.

Haka kuma a shekarar 2021 ma ƙasashen biyu sun shafe watanni masu yawa suna ce-ce-ku-ce game da harkar sufurin jiragen sama.

Leave a Reply