Na shiryar tsaf don daidaita sahun mambobin ƙungiyar masu maganin gargajiya a jihar Yobe – Alhaji Ado

0
131

Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu

A ƙoƙarin dawo da martabar ƙungiyar masu maganin gargajiya (NANTMP) a jihar Yobe sabon shugaban riƙo na ƙungiyar, Alhaji Ado Yaro mai maganin Gargajiya kuratandu Gashuwa ya bayyana cewar a halin da ake ciki ya shiryar tsaf don daidaita sahun ƙungiyar, sakamakon tafiyar da a baya ta ke yi ba bisa bin hanyoyin da suka dace ba.

Alhaji Ado ya bayyana hakan ne a tattaunawar sa da wakilinmu a garin Damaturu dangane da yadda ya ke ga matsalar ƙungiyar jim kaɗan da karɓar iagoranci daga tsoffin shugabannin ta kafin gudanar da zaɓe nan gaba. Ya ƙara da cewar, a matsayin sa na shugaban riƙo na wannan ƙungiyar a jihar Yobe ya ɗaura ɗamarar ganin an inganta wannan ƙungiyar ta masu maganin gargajiya a jihar ta yadda shi da sauran shugabannin riƙo za su yi duk abin da za su iya yi don ganin sun daidaita sahun mambobin da kuma ita kanta ƙungiyar don komawa cikin hayyacin ta daga doguwar sumar da ta yi a baya.

“Alhaji Ado ya ƙara da cewar, duk da cewar ba’a daɗe da rushe tsoffin shugabannin wannan ƙungiyar ba, amma duk da haka a ganin sa an san zai iya ne ya sanya mambobin ƙungiyar da masu ruwa da tsakiya na ƙungiyar suka ɗauko ni don ɗora min alhakin riƙe wannan ƙungiyar har kaiwa ga lokacin da za’a sake zaɓo sabbin shugabannin da za su shugabancin ƙungiyar kamar yadda tsarin Mulkin ta ya ke.”

Da wakilinmu ke tambayar sa akan ko wane hoɓɓasa zai yi don ganin ya ɗora wannan ƙungiyar ta su kan tafarkin da ya dace? “A nan sai ya kaɗa baki ya ce,  a halin da ake ciki shi da sauran sabbin shugabannin ƙungiyar suna hoɓɓasa don ganin sun za ga dukkannin ƙananan hukumomin jihar 17 don ganawa da mambobin wannan ƙungiyar da nufin ganawa da su don wayar musu da kai yadda za su tsarkake wannan sana’a ta sayar da maganin gargajiya tare da faɗakar da su ta yadda za su riƙa sarrafa magungunan ba tare da kaucewa hanyar ba ko kuma gurɓata shi ba lura da cewar al’umma ne ke amfani da shi don samun waraka.”

KU KUMA KARANTA: Ko kasan maganin ciwon haƙori sadidan?

Shugaban ya kuma ƙara da cewar babban abin da ya ƙara mana ƙarfin gwiwar wannan ziyarce-ziyarce da suka shirya yi ga ƙananan hukumomin jihar shi ne don ƙoƙarin tantance yawan mambobin da muke da shi kamar yadda hukumar lafiya ta jihar Yobe ta bamu shawarar yi don sanin yadda za mu yi rijistar kowane mamban wannan ƙungiyar don tafiya daidai da zamanin, lura kuma da cewar hukumar lafiya ta jihar na da shirin samar da ƙudirin buɗe ɓangaren masu maganin Gargajiya a wasu asibitoci uku da ke jihar wadda kan hakan ne ma muka bazama don tantance adadin mambobin mu.

“Haka nan za kuma mu bi hanyoyi don sake daidaita sahun masu maganin gargajiya a jihar ta Yobe yadda za mu sa dokar daina tallar magani ta yadda wasu ke ƙure sautin amsa kuwa ta yadda ake riƙa damun mutane da ƙarar amsa kuwa (Loudspeaker) fiye da ƙima da kuma yawaitar furta maganganun batsa yayin tallar maganin a tituna da kasuwanni da kuma wuraren taruwar jama’a da makamantan haka. “

“Don haka mun ƙudiri aniyar cikin ikon Allah a ƙarƙashin wannan shugabanci namu na riƙo za mu yi duk abin da za mu yi don ganin mun ɗora wannan ƙungiyar ta mu ɗoɗar akan hanya don ganin mun shiga cikin samun sauran ƙungiyoyin masu maganin gargajiya da ke jihohin ƙasar nan ta kowace fuska kuwa.”

“Shugaban ya kuma ba da tabbaci ga gwamnatin jihar ta Yobe cewar, za su bi dukkannin dokokin da gwamnatin ta gindaya ga masu maganin gargajiya don ganin mambobin ƙungiyar ba sa wuce gona da irin a yayin gudanar da wannan sana’a ta su ta maganin gargajiya kuma sun saba kayar ladabtar da duk wani mamban ƙungiyar da ya karya dokokin kungiya da kuma dokokin gwamnati.”

Leave a Reply