Mutum 19 sun mutu sakamakon haɗarin mota a garin Abuja

An tabbatar da mutuwar mutum 19 a wani mummunan haɗarin mota a da ya auku a kan hanyar Yangoji zuwa gwagwalada a Abuja babban birnin Najeriya.

Da yake tabbatar wa da kamfanin dillacin labaran ƙasar NAN adadin waɗanda suka mutun, mai riƙon kwaryar babban kwamandan hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa, Mista Dauda Biu, ya ce hatsarin ya rutsa ne da motoci uku.

Ya ƙara da cewa hatsarin ya rutsa da mutum 31, inda mutum takwas suka samu munanan raunuka, yayin da kuma 19 suka mutu.Ya ce bincike ya nuna cewa gudun wuce-kima tare da neman wuce juna ne ya haddasa aukuwar hatsarin.

Ana dai yawan fuskantar haɗuran mota a manyan titunan Najeriya, wanda ake ɗora alhakin hakan kan rashin kyawun tituna, da tuƙin ganganci, da uwa uba gudun da ya wuce kima, da masu ababen hawa ke yi.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *