Muna Da Hujjoji Na Arangizon kuri’u A Zaɓen Shiyyar Kaduna Ta Tsakiya Na PDP – Inji Lauyan Sardaunan Badarawa

0
744

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

LAUYAN Dan takarar Kujerar Sanata a Shiyyar Kaduna ta tsakiya, Honarabul Usman Ibrahim, wanda aka fi sani da Sardaunan Badarawa, wanda ya fafata a zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP da aka kammala domin zaben 2023 mai zuwa, ya bayyana cewa yana rike da hujjojin faifan bidiyo da ke nuna yadda wakilai suka kada kuri’a da arangizon da aka yi a matsayin hujja.

Wani Babban Lauyan Najeriya (SAN), Samuel Atung ne ya bayyana haka a wata hirar da ya yi da manema labarai a babban kotun tarayya dake Kaduna.

Lauyan ya bayyana cewa zaben fidda gwanin da ya samar da Lawal Adamu (Mr. LA) a matsayin dan takarar jam’iyyar PDP na Kaduna ta tsakiya, an tafka kura-kurai da arangizon wasu Kuri’u.

Ya kara da cewa wanda yake karewa yana rike da hujjojin faifan bidiyo da na hoton da ke nuna yadda wakilai suka kada kuri’a wadanda sakamakon shari’ar da ya yi nuni da cewa sun ruguza sakamakon zaben fidda gwani.

“Bayan jam’iyyar PDP ta Kaduna ta tsakiya ta tsayar da dan takararta a matsayin dan takarar zaben 2023, wanda shi da muke karewa ya rubuta koke ga kwamitin daukaka kara na jam’iyyar yana kalubalantar sakamakon zaben, mun shigar da karar kotu.

“Muna da hujjojin faifan bidiyo a kan haka kuma kwamitin ta yi la’akari da koken da muka yi tare da mika shawararsa ga kwamitin (CWC) wanda a hikimarsa ya bukaci a sake zaben fidda gwani.

“Jam’iyyar PDP ta rubuta wa INEC wasika, inda ta sanar da ‘yan sandan Najeriya, jami’an tsaron farin kaya da sauran masu ruwa da tsaki kan matakin da ta dauka na sake gudanar da zaben fidda gwani na shiyyar Sanata Kaduna ta tsakiya, wanda abin farin ciki ne sai ba a yi hakan ba.”

“Abin takaici a ranar da aka saka za ayi zaben, shi wanda muke karewa ya tattaro magoya bayansa zuwa wurin da za a sake zaben fidda gwanin, sai aka ce ba za a sake gudanar da zaben ba saboda yadda Jam’iyyar ta tsara kenan.

“Mun zo kotu ne a yau (Juma’a) muna neman a tilasta wa jam’iyyar PDP ta mika sunan kowane dan takara domin tabbatar da gaskiya da adalci a zaben 2023 har sai bayan an sake zaben fidda gwanin.

“Dukkanmu mun san illar da shari’a ta haifar da wuce gona da iri kamar yadda aka bayyana karara a hukunce-hukuncen shari’a wanda ke da yuwuwar bata sakamakon zabe da tsari.

“Mun rigaya mun zayyana matsayinmu a gaban kotu wanda hakan ya sa lamarin ya zama abin yi har sai kotu ta yi la’akari da hukunci.

“A yau ne maganar ta ke, muna da kudirin dokar hana PDP mika sunan kowane dan takara ga INEC har sai an sake zaben fidda gwani.

“Abin takaici kotun ba ta zauna a yau ba, Alkalin kotun, Mai shari’a Muhammad Garba Umar ya dage sauraron karar zuwa ranar 20 ga watan Yuni 2022,” inji shi.

Leave a Reply