Mun Yi Farin Ciki Da Sake Bude Iyakokin Kan Tudu A Najeriya

0
361

Daga; Rabo Haladu.

MAZAUNA garuruwan da ke kan iyakokin Najeriya da aka rufe na ci gaba da bayyana farin cikinsu bayan da Gwamnatin ta yanke hukumcin sake buɗe iyakokin da ke kan tudu a ranar Litinin.

Hukumar hana fasa-ƙwauri ta ce gwamnatin tarayya ce ta ba da umarnin buɗe iyakokin huɗu a ƙarshen makon jiya.

An dai amince a bude iyakokin Idoroko a Jihar Ogun da Jibiya dake Jihar Katsina sai kuma iyakar Kamba a Kebbi da kuma iyakar Ikom a Jihar Cross River.

Bayan bude iyakar Jibiya a Katsina, mutanen da ke yankin sun bayyana jin dadinsu kasancewar harkokin kasuwanci zai farfado a cewarsu.

Alhaji Salisu O I Jibiya, ya shaida cewa, bude iyakokin nan ya sanya su cikin jin dadi da raha saboda sun shafe shekaru uku suna rufe abin da ya sanya su cikin takura.

Ya bayyana cewa duk da ka’idojin da hukumomi suka gindaya musu na irin abubuwan da za a rinka safararsu ta iyakokin, su kam sai san barka saboda koba komai za su ci gaba da kasuwancinsu da suka jima basa yi.

Alhaji Salisu O I Jibiya, ya ce ” A yanzu an yarda mu shigo da abubuwa da suka hada da wake da aya da kuma dabino, amma duk sai mun biya kudin fito.”

Yahuza Sahabi, mazaunin garin Kamba ne inda aka bude iyakar, ya kuma shaida cewa, bude iyakar nan shi ne babban alfanu garesu, domin za su samu saukin farashin kayayyaki musamman na abinci.

Ya ce,” A gaskiya mu mutanen da ke rayuwa a garuruwan da ke kan iyaka, rufe su ya yi matukar taba mana rayuwa musamman ta fuskar tattalin arziki.”

Yahuza Sahabi, ya ce a lokacin da aka rufe iyakarsu sun ga kalubale kala-kala, saboda yadda farashin kayan abinci ya tashi sosai, ba karamin kuncin rayuwa suka shiga ba.

Ya ce, amma a yanzu tunda an bude iyakar, farashin kayan abinci da ma sauran kayan bukatun yau da kullum zai sauko.

Hukumomin Najeriya dai sun sha fada cewa, rufe iyakokin ya taimaka wajen bunkasa harkokin masana’antun cikin gida da noma musamman na shinkafa.

A karshen shekarar 2020 ne, shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin bude iyakokin kasar hudu na kan tudu da suka hada da Semi da Ilela da Maigatari da ku ma Ofong.

A watan Agustan 2019 ne gwamnatin kasar ta rufe iyakokin nata da zummar daƙile yawaitar fasa-kwauri da kuma bunƙasa tattalin arziki, ko da yake ‘yan kasar da dama sun koka kan matakin.

Hukumar hana fasa-ƙwauri, wadda ta yi ruwa ta yi tsaki wajen ganin an yi aiki da rufe iyakokin, ta bugi ƙirji game da irin nasarorin da ƙasar ta samu saboda matakin da ta dauka na rufe iyakokin tudu ta fuskoki daban-daban na rayuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here