Mun bada isasshen lokaci don haka babu ja da baya kan daina karɓar tsoffin kuɗi- CBN

3
400

Babban bankin Najeriya ya dage kan cewa babu gudu babu ja da baya a ranar 31 ga watan Junairu na wa’adin tsofaffin takardun kuɗi na Naira 200, 500 da 1,000, domin kuwa zmefiea su daina karɓarsu a kasar.

Gwamnan babban bankin na CBN Godwin Emefiele ya sake nanata matsayin babban bankin bayan taron kwamitin kula da harkokin kuɗi a Abuja ranar Talata.

Emefiele ya kuma dage kan cewa an bai wa ‘yan Najeriya isasshen lokacin da za su musanya tsofaffin takardun naira da sababbi.

Hakan na zuwa ne kamar yadda kuma ya ce sace mutane da karbar kuɗin fansa ya ragu tun bayan da aka sake fasalin takardun kuɗi guda uku.

Sai dai ‘yan Najeriya da dama sun koka kan rashin samu da ƙarancin sabbin takardun, inda suka nuna rashin amincewarsu da cewa har yau bankunan na baiwa kwastomomin tsofaffin takardun naira da wa’adin kwanaki kadan ya rage.

KU KUMA KARANTA:CBN zai hukunta duk bankunan da ke ɓoye sabbin kuɗi

A halin da ake ciki, CBN a ƙoƙarinsa na tabbatar da cewa kowa ya shiga shirin musanya kuɗi a faɗin ƙasar domin baiwa waɗanda ke yankunan da ba su da banki damar yin musanyar tsofaffin takardunsu kafin wa’adin ranar 31 ga watan Janairu, amma ban da kuɗin wayar hannu na Legas da Abuja.

Haka kuma a kwanakin baya CBN ya umarci bankunan kasuwanci da su gaggauta daƙatar da fitar da sabbin takardun kuɗi ba bisa ka’ida ba tare da loda injinansu na ATM da takardun kuɗin Naira da aka sake fasalin domin bunƙasa yaɗuwa.

Sai dai duk da ƙoƙarin da babban bankin ya yi, abokan hulɗar bankin na ci gaba da kokawa kan ƙarancin sabbin takardun kuɗi.

A ranar Talata ne majalisar wakilai ta gayyaci bankunan kasuwanci kan karancin sabbin takardun kuɗi na naira.

Manajan daraktoci, babban jami’an bankuna, a karkashin kwamitin ma’aikatan bankuna, za su gana da kwamitin wucin gadi na majalisar wanda shugaban masu rinjaye, Alhassan Ado-Doguwa, zai jagoranta a ranar Laraba 25/01/23.

Majalisar ta kuma yanke shawarar cewa za a tsawaita tagar musanya tsofaffin takardun da sababbi da wata shida.

A halin da ake ciki, majalisar dattawa a ranar Talata ma ta yi kira ga babban bankin ƙasar da ya ƙara wa’adin watanni shida shi ma, daga ranar 31 ga watan Janairu zuwa 31 ga Yuli, 2023.

A ranar 26 ga Oktoba, 2022 ne CBN ya bayyana shirinsa na sake fasalin takardun kuɗi guda uku, daga nan ne shugaban ƙasa,Muhammadu Buhari, ya ƙaddamar da sabbin takardun kuɗi na N200, N500 da N1,000 a ranar 23 ga watan Nuwamba, 2022, yayin da babban bankin ya sanya ranar 31 ga watan Janairu domin tabbatar dai na karɓar tsoffin takardun.

3 COMMENTS

Leave a Reply