Ministocin harkokin wajen Najeriya da Rasha sun tattauna kan zaman lafiyar yankin Sahel

0
66

Ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Maitama Tuggar da takwaransa na Rasha Sergey Lavrov sun tattauna batutuwan da suka shafi moriyar juna da kuma zaman lafiyar yankin a birnin Moscow ranar Laraba.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X wadda a da aka fi sani da Twitter, Tuggar ya ce ganawarsa da Lavrov na ƙara ƙarfafa dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu, musamman a fannin bunƙasar tattalin arziƙi da samar da zaman lafiyar yankin Sahel.

“Dangantakar Najeriya da Rasha na da daɗaɗen tarihi, wanda ke da nasaba da haɗin gwiwa a fannoni daban-daban da suka haɗa da diflomasiyya, kasuwanci, da tsaro. A cikin shekarun da suka gabata, ƙasashen mu sun yi aiki tare a kan batutuwan da suka shafi moriyar juna, tare da ƙarfafa dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu.” Inji Tuggar.

“Ganawar da na yi da ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov, na ƙara ƙarfafa wannan dangantaka ne, musamman a fannin bunƙasar tattalin arziƙi da samun zaman lafiyar yankin.

Tattaunawarmu ta mayar da hankali ne kan inganta haɗin gwiwa don bunƙasa tattalin arziƙi a Najeriya da tabbatar da zaman lafiya a yammacin Afirka da yankin Sahel.”

KU KUMA KARANTA:Wata mata ta ɗauki nauyin kuɗin makarantar masu koyon aikin haɗa magunguna a New York

Tuggar ya kuma ce dage takunkumin da Rasha ta ƙaƙaba wa Burkina Faso, Mali da Nijar, ya ƙara jaddada aniyarta na tallafawa ayyukan tsaro a yankin, ciki har da ƙungiyar ECOWAS ta yammacin Afirka.

“An kuma amince da muhimmiyar rawar da Najeriya ke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin, tare da yin ƙira da a ƙara ba da taimako daga ƙasar Rasha don magance ƙalubalen tsaro.

“Waɗannan tattaunawa sun yi daidai da manyan manufofin dangantakar da ke tsakanin ƙasashen Najeriya da Rasha, tare da jaddada muhimmancin haɗin gwiwa wajen tunkarar ƙalubalen da ake fuskanta da kuma inganta ci gaban juna.

“Sun kafa harsashin tuntuɓar juna a nan gaba da kuma ziyarar da za a iya yi a nan gaba, ciki har da wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai kai birnin Moscow, wanda ke nuna aniyar ƙasashen biyu na zurfafa dangantakarsu,” in ji ministan na Najeriya.

Leave a Reply