Mecece sana’ar fawa?

0
840

Mahauta sukan samu abin yanka daga Fulani. Sai su je wurin Bafulatani su karɓo Karsana ko Bijimi ko Guzuma (Saniya wadda ta tsufa), sai su kawo ta gida, su turke ta ta yi ƙiba, don ta yi mai.

Sai su kai ta mayanka, malami mai yanka ya yanke ta. Su kuwa runji, su kauda ta waje ɗaya, su feɗe ta, watau; Su raba ta da fata.

Sannan, sai su fasa cikin su yaye ‘yan ciki sarai, su tumbi, su tumburƙuma, su hanji, su bamayaƙa, da sauran su. Akwai maɗaciya wadda in ba a fitar da ita ba sai ‘yan ciki su yi ɗaci, daɗa balle hanta, da huhu da zuciya, waɗannan ba za su ciwu ba, don sun fi kusa.

Bayan wannan kuma, sai a bi nama a yanke shi gaɓa-gaɓa, a fitar da cinyoyi da karfatu da awazai da wuya da kai. Sannan sai su bi su ɗebi tsoka waje ɗaya, duk su ƙwalƙwale ƙashin duka, su bar shi babu mamora, mai saura ‘yar-tsoka shi su kwankwatsa shi da gatari ko adda, to, duk haka za su sayar da shi, mai son ƙashi su ba shi, mai son tsoka su ba shi.

KU KUMA KARANTA: Matasa Ku Nemi Ilimin Koyon Sana’a – Ustaz Takwashe

Akwai masu tsire, sai su zo wurin danginsu su sara, su je su yanka gutsun-gutsun su tsire su a jikin tsinkunansu, su jera su ga tukuba su kawo itace su hura wuta a coka naman, har naman nan ya gasu, a barbaɗa masa yaji da mai da guru, sai a sa cikin baka (ƙwarya mai faɗi) a je a yi talla a saida.

Wasu kuma sai su sara su yi kilishi, wato su reɗe nama ya yi faɗi, sannan su shanya shi ya bushe, sannan su kawo yaji da gishiri da jangargari, su tushe shi luƙui, su niƙa shi ya yi gari lis, su kwaɓa, su tsoma naman nan busashshe.

Sannan, su ɗebe su ƙara shanyawa, ya bushe tare da abubuwan nan, to ya zama kilishi sosai kenan, sai a saida ‘yan ƙanana ɗari-ɗari, igiya kuwa mai faɗi kuɗinta taro ne.

Leave a Reply