Mawallafin jaridar Neptune Prime ya gina makaranta da asibiti a Yobe (Hotuna)

0
186
Mawallafin jaridar Neptune Prime ya gina makaranta da asibiti a Yobe (Hotuna)

Mawallafin jaridar Neptune Prime ya gina makaranta da asibiti a Yobe (Hotuna)

Daga Ibraheem El-Tafseer

Mawallafin jaridar Neptune Prime, Dakta Hassan Gimba ya gina makaranta da asibiti a garin Potiskum jihar Yobe. Bukin buɗe makarantar ya gudana ne a harabar makarantar da ke unguwar Jaji, a ranar Asabar.

Makarantar ta ƙunshi ɓangaren Nursery ne daga aji ɗaya zuwa aji uku. Sai kuma ajin firamare ɗaya (primary one). Iyakacin karatun da za a fara da shi kenan, kafin gaba.

A nasa jawabin a wajen, Dakta Gimba, ya fara ne da godewa Allah (T) da ya kawo mu wannan rana. Ya ce “farin ciki na ba zai misaltu ba. Tun daga jama’ar da na gani a wajen ɗaurin aure ɗana, da kuma irin jama’ar da na gani a nan, na rasa ma ta ina zan fara nuna farin ciki na, da kuma godiya jama’a”.

Gimba ya ci gaba da cewa “babu abin da ya fi farin ciki, irin ka ga ka saka mutane a cikin farin ciki. Lokacin rasuwar Mama (Hajiya Hafsat), sai na ga me zan yi da sunanta wadda zai saka mutane a cikin farin ciki, to shi ne na ga gina makaranta da sunanta zai fi.

Da a tunani na, Islamiyya za mu gina, to sai muka tattauna da wani aminina, abokina Abubakar Monja, (Allah ya masa rasuwa) da shi ne muka yi shawarar a gina makaranta ɗin. Akwai ɗakin na’ura mai ƙwaƙwalwa (kwamfuta) da muke gina wa, idan aka kammala sunansa za mu saka, Abubakar Monja”.

KU KUMA KARANTA: Mawallafin Neptune Prime zai ƙaddamar da asibitin cutar kansa, makaranta, da gidauniyar tallafi a Yobe

Sannan an wuce duba Asibitin ‘cutar kansa’ da yake gina wa, domin tuna wa da marigayiya matarsa, wadda aka saka wa asibitin sunanta Hajiya Lami Babare Clinic.

Dakta Gimba ya bayyana gina asibitin domin taimakon al’umma da suke wannan yanki. Sannan al’ummar yankin suna ta murna da farin ciki da samun asibitin. Sun ce yanzu kam nesa ta zo kusa, ganin yadda suke nesa matuƙa da babban asibitin garin Potiskum.

Mutane da dama ne suka halarci wajen, sun haɗa da wakilin mai martaba sarkin Fika, Alhaji Bukar Abubakar, Shettiman Fika, Hakimi Shayibu (Hakimin Lai Lai), Dakta Mamman Mohammed, Shamakin Fika, Dakta Mamman Mamuda (shugaban kwamitin amintattu na makarantar), Farfesa MK Othman (tsohon Darakta NAERLS, na Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, Mista Iliya Joshua (mai magana da yawun hukumar Kwastam ta ƙasa, reshen Borno da Yobe. Da sauran ɗimbim al’umma da suka halarci wannan taro.

Kalli hotunan a nan:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here