Matashin da ya ceto Fasinjojin Jirgin Saman da yayi Hatsari a Tanzaniya ya samu gagarumar kyauta

An karrama wani matashi mai sana’ar kamun kifi a matsayin gwarzo a Tanzania tare da ba shi kyautaar shillings miliyan 1 kwatankwacin Dala dubu 430 bisa jarumtar da ya nuna wajen ceto mutanen da suka makale a jirgin saman da ya yi hatsari a ƙasar a ƙarshen makon jiya.

Majaliwa Jackson wanda tuni gwamnatin Tanzania ta ba shi aiki kai tsaye a Hukumar Kashe Gobara ta ƙasar, ya bayyana irin wahalar da ya sha a yayin ƙoƙarinsa na ceto matukan jirgin da suka maƙale, inda ya ce, ƙiris ya rage ya rasa ransa.

Jim kaɗan da faɗuwar jirgin cikin tafkin Victoria a ranar Lahadi, Jackon tare da wasu masunta uku, suka doshi wurin da hatsarin ya auku, inda suka yi amfani da filafilin kwale-kwale wajen fasa kofar baya na jirgin tare da ceto tarin fasinjoji.

Mutane 24 daga cikin fasinjojin jirgin 43 suka tsira da ransu, yayin da 19 suka rasa rayukansu a hatsarin jirgin na kamfanin Precision Air mafi girma a Tanzania.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *