Matashi ɗan shekara 15 ya kashe abokinsa akan ƙwallon sunuka

Daga Shafa’atu DAUDA, Kano

Wani matashi mai kimanin shekara 15 ya soki abokinsa da wuƙa a yayin wata takaddama, hakan kuma ya zama ajlinsa.

Lamarin ya faru ne a ƙaramar hukumar Rimin Gado a Jihar Kano a ranar Juma’a, inda matasan suka samu sabani a wajen wasan kwallon Sunuka.

A cewarsa, marigayin ne a lokacin takaddamar ya ƙalubalance shi da idan ya isa ya zo su je bayan gari domin a raba raini.

Shi kuma da ya tashi zuwa sai ya tafi da wuƙar da yake yankar rake wacce ya soki abokinsa da shi.

“Muna zuwa sai ya shake ni, ya kama ni da duka, ni kuma da na ga haka, sai na fito da wukar na caka masa a kirji,” in ji matashin.

An garzaya da Musbahu zuwa Asibitin Murtala na cikin birnin Kano, a inda suna zuwa, ko fita da shi daga mota ba a yi ba rai yayi halinsa, da likita ya duba shi, ya ce ya mutu, in ji kawun marigayin.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, SP Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar al’amarin.


Comments

2 responses to “Matashi ɗan shekara 15 ya kashe abokinsa akan ƙwallon sunuka”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Matashi ɗan shekara 15 ya kashe abokinsa akan ƙwallon sunuka […]

  2. […] KU KUMA KARANTA: Matashi ɗan shekara 15 ya kashe abokinsa akan ƙwallon sunuka […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *