Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano
Daga Jameel Lawan Yakasai
Al’ummar unguwar Hotoro Maraɓa sun wayi gari da tashin hankali bayan wani matashi ya kashe ladanin masallacin unguwar da asubar yau Litinin.
Rahotanni daga mazauna unguwar sun bayyana cewa matashin ya zo yin sallah sai ya iske ladanin da wasu mutane uku daga nan ne ya bayar da umarnin da tayar da sallah, shi kuma ladan ya bayyana masa cewar lokaci bai ƙarasa ba.
Daga nan ne matashi ya zaro wuƙa daga aljihunsa ya soka wa ladanin a maƙogwaro harma aka yi zargin ya cire maƙogoron marigayin ya sanya a leda.
KU KUMA KARANTA: Matashi a Kano ya kashe abokin sa saboda yana yawan tashinsa Sallar Asuba
Wannan ya sa ’yan unguwar kamo shi tare da lakaɗa masa duka har ya ce ga garinku nan.
A halin yanzu jami’an ’yan sanda na jihar Kano na unguwar domin kwantar da tarzomar da ke shirin ɓarkewa bayan matasan unguwar sun yi dandazon a ƙofar gidan matashin da nufin ƙonewa.