Matashi ya rasa ransa sakamakon faɗawa cikin tankin diesel a Kano

1
860

Daga Shafa’atu DAUDA Kano

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta samu nasarar ceto wani matashi da ba’a San ko wanene ba daga cikin tankin man diesel na sabis antenna ɗauke da galan cikin mawuyacin hali.

Neptune prime ta rawaito lamarin ya faru ne a gaida kuka uku dake ƙaramar hukumar Kumbotso. Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Kashe Gobara ta Jihar kano Saminu Yusuf Abdullahi shi ne ya shaida hakan ga Manema Labarai, Inda yace tun a daren jiya da misalin ƙarfe uku da minti talatin suka samu kiran gaggawa ta bakin jami’in su Mai suna Ibrahim Mukhtar Bicci.

Ya ƙara da cewa jami’an su sun Isa inda lamarin ya faru suka kuma iske matashin ɗan shekaru talatin da biyar acikin Tankin Diesel, sai dai jami’an tsaron inda Abun ya faru suma sun tabbatar da cewa basu San matashin ba.

Koda yake bayan ceto matashin cikin mawuyacin hali daga bisani aka samu tabbacin rasuwar sa. Bayan da aka miƙa shi zuwa ga hannun jami’an hukumar ‘Yan sanda mai suna insufeto Elisha bulish dake aiki a ofishin ‘Yan sanda dake fanshekara Kawo yanzu dai PFS Saminu Yusuf yace basu tabbatar da musabbabin faruwar iftila’in ba.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here