Matasa a Imo sun kama ɗan sanda bisa zargin sace ƙuri’un zaɓe

0
195

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce za ta gudanar da bincike kan zargin tafka maguɗi a zaɓen da aka yi wa ɗaya daga cikin jami’anta a jihar Imo.

Bidiyon wani jami’in da wasu matasa ke riƙe da shi da suka zarge shi da sace ƙuri’a a cibiyar tattara ƙuri’u ta Amakohia Ikeduru a lokacin zaɓen gwamna da aka yi a ranar 11 ga watan Nuwamba.

Da yake mayar da martani ga faifan bidiyon, kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya ce;

‘’Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta na sane da zargin da ake yi wa wannan ɗan sanda da ake zargin yana da hannu wajen sace ƙuri’u a cibiyar tattara ƙuri’u ta Amakohia Ikeduru da ke jihar Imo. 

KU KUMA KARANTA: ’Yan daba sun buɗe wa masu zaɓe wuta a Bayelsa

Ba mu ɗauki wannan batu da wasa ba domin yana damun sahihancin rundunar da kuma yadda mambobinta za su iya tabbatar da ingancin zaɓe. 

Don haka muna tabbatar wa jama’a cewa za a gudanar da cikakken bincike, kuma za mu yi muku bayani nan da nan.  Yana buƙatar cikakken bincike.

Leave a Reply