Matar da ke tunƙaho da gashin-bakinta

0
501

Daga Fatima GIMBA, Abuja

Masu ziyartar shafukan sada zumunta da muhawara na nuna sha’awa da kuma yabo yayin da wasu ke nuna kyama ga wata mata ‘yar Indiya wadda ke da baiwar gashin-baki.

Sai dai duk da yadda wasu ke mata zambo da shaguɓe ita kam ta ce ko a jikinta, hasali ma tana son wannan baiwa ta fuskar tata.

Shyja

Shyja mai shekara 35 ta rubuta a shafinta na WhatsApp bangaren hotonta cewa, ”Ina ƙaunar gashin-bakina.”

Yawancin mutanen da suka hadu da ita a Facebook ko kuma suka ganta a zahiri sukan tambaye ta dalilin da ya sa take barin gashin-bakin, har ma take ado da shi.

“Abin da nake gaya wa mutane kawai, shi ne, ina son abuna sosai,” in ji ta.

Shyja, wadda ke amfani da suna daya kawai tana zaune ne a gundumar Kannur a jihar Kerala da ke arewacin kasar ta Indiya.

Harnaam Kaur, me fafutuka ‘yar Birtaniya ta faɗa tana gwagwarmaya kan barin kowa yayi adon ji jikinsa yadda yakeso

Ita ma kamar sauran wasu mata ta dade da wannan gashin-baki.

Duk da cewa tana rage girarta akai-akai, Shyja ta ce, ita ba ta taba tunanin wai ta aske gashin-bakinta ba.

Kusan shekara biyar da ta wuce sai gashin ya riƙa fitowa sosai kamar na namiji, wanda hakan ya ba ta sha’awa sosai, har ma ta ce bari ta bar shi kamar yadda na maza yake.

”Bana ma taɓa tunanin yadda zan ci gaba da rayuwa ba tare da wannan gashin-bakin ba.

Lokacin da aka fara annobar korona, ba na son sanya takunkumi kodayaushe saboda yana rufe min fuska,” in ji ta.

Mutane da yawa idan suka ganta sai su ce mata ta aske shi, amma ta ƙi.

Ta ce, ”Ban tana jin cewa ni ba kyakkyawa ba ce saboda ina da wani abu da bai kamata a ce ina da shi a jikina ba.”

“Yawanci ana gaya wa mata cewa bai kamata su bar gashi a fuskarsu ba, na shawartarsu da su je su biya a aske musu ko kuma a gyara musu shi yadda zai yi kyau kodayaushe,” in ji ta.

Akwai mai da sauran abubuwa na aske ko fitar da gashi ko kuma gayra shi masu tsada, wadanda musamman na mata ne wadanda a su iya saye.

To amma a ‘yan shekarun nan mata da yawa sun yi watsi da wannan al’ada ta aske gashin da ke fitowa a wani sashe na fuskarsu, har ma alfahari suke yi da shi.

A shekara ta 2016, mai rajin kare ‘yancin gyara jiki Harnaam Kaur ta kasance matashiyar mace ta farko a duniya da ta tsayar da gemu cikakke kamar namiji, in ji littafin tattara bajinta na duniya (Guinness World Records).

A wajen Shyja, barin gashin-baki ba wai nuna wata manufa ba ce, illa kawai halitta ce da jikin mutum yake da ita, wadda za a gani a san yadda kake.

Ta ce “Ni ba abin da ya dame ni ina rayuwata ne yadda nake so Idan da rai biyu gare ni, da watakila sai na bar wa wasu su yi daya rayuwar.”

Wasu daga cikin irin wadannan abubuwan suna samun mutum ne idan ya gamu da larura ta tsawon shekaru.

An yi wa Shyja tiyata har sau shida a cikin shekara goma – daya an fitar mata wani kumburi ne a nononta, wata kuma an cire mata wani kari ne a mahaifarta.

Tiyata ta karshe da aka yi mata shekara biyar da ta gabata, an cire mata mahaifa ne.

“Duk lokacin da aka fito da ni daga dakin tiyata, fata nake a ce ba za a sake shiga da ni ba,” in ji ta.

Ganin bayan matsaloli na lafiya iri daban-daban ta Shyja ta yi ba abin da hakan ke sa ta sai dai samun kwarin guiwa na ta yi rayuwarta yadda take so.

Shyja ta ce tana da kunya sosai lokacin tana ‘yar karama.

Ba kasafai ake ganin mata a waje ba a kauyensu bayan karfe shida na dare.

Duk da cewa Kerala na daya daga cikin jihohin Indiya da suka fi ci-gaba, to amma har yanzu al’adar maza su mamaye komai ita ake yi a yawancin wurare.

Kuma galibi ba a son mata su rika tafiye-tafiye ko kuma zama su kadai.

Lokacin da ta yi aure ta koma jihar Tamil Nadu, mai makwabtaka da su, Shyja ta ce sai ta ji dadin irin rayuwar da ta samu kanta a ciki.

Kamar ta samu wani sabon ‘yanci da walwala.

“Mijina zai tafi aiki sai can dare zai dawo. Saboda haka da yamma sai in fito kofar gida na zauna. Wani lokaci ma sai na je shago ni kadai da daddare na sayo kaya idan ina bukata.

Ba wanda ya damu. Yadda ya kasance na fara yin abubuwa ni kaɗai, abin ya sa na samu kwarin guiwa a rayuwata.”

Ta kara da cewa, ” Yanzu irin wannan al’ada nake so na koya wa ‘yata.”

Iyaye da dangi da kuma kawayen Shyja suna ba ta goyon baya a kan son gashin-bakin da take yi.

A lokuta da dama ‘yarta kan ce mata gashin-bakin ya yi mata kyau.

Amma kuma Shyja ta ce ba irin maganganun da mutane ba sa gaya mata idan suka hadu da ita a titi.

“Mutane na yi min dariya, suna cewa ‘maza ne da gashin-baki, ya mace kuma take da shi?'” in ji ta.

A shekarun baya, a lokuta da dama an yi ta nuna ta da yin rahoto da shiri a kanta a kafafen yada labarai na kasar.

A baya-bayan nan, ta ce ta ga maganganu da sakonni da aka yi ta yi a kan wata makala da aka rubuta a kanta.

Ra’ayoyin da wata kafar yada labarai ta sanya a shafinta na Facebook.

Wani daga cikin masu bayyana ra’ayin nasu, ya ce, ”Me ya sa ba za ta aske gashin-bakin nata ba, tun da har tana dan aske girarta ta gyara ta.

“To amma wannan ba ra’ayina ne na barin abin da nake so a jikina da kuma abin da bana so ba?” Ta tambaya.

Yawanci kawayen Shyja suna mayar da kakkausan martani a kan wadannan ra’ayoyi na Facebook, amma ita cewa take abin ba ya damunta ko kadan.

“Hasali ma wani lokaci kallonsu kawai nake na yi dariya.”

Leave a Reply