Mata da ƙananan yara 11 sun rasu a hatsarin mota a Kano

Aƙalla mata da yara 11 ne aka ruwaito sun mutu a wani hatsarin mota da ya afku a hanyar Kano zuwa Zariya, hatsarin wanda ya auku da yammacin ranar asabar da misalin karfe 5 na yamma, ya haɗa da wata motar bas kirar Toyota C20 da wata motar bas ƙirar Hilux.

Wani ganau ya shaida cewa, “Motar Hilux da ta taho daga Kano zuwa Zariya tana bin motar daga baya da gudu, tana so ta wuce bas ɗin, sai ga wata mota tana zuwa, wanda hakan ya sa direban ya ja da baya.

KU KUMA KARANTA:Mutane 37 sun mutu a hatsarin mota tsakanin Damaturu zuwa Maiduguri

“Lokacin da direban na Hilux ya ja baya,sai kawai ya hau motar kirar Toyota daga baya, ya sa ta faɗa kan titin sannan ta kama da wuta.

“Baya ga mutane shida da suka tsira, mun kirga gawarwaki goma sha ɗaya da gobarar ta kone, kuma dukkansu mata ne har da kananan yara,” in ji shi.

A zantawar jaridar Daily trust Malam Abdul-Aziz Isyaku, wanda ya rasa ‘ya’ya mata biyu – Zainab ‘yar shekara 16; da Aisha, mai shekaru 8 – ya ce marigayan na komawa Zariya ne daga Kano bayan sun ziyarci ‘yan uwansu.

“Muna jiran su a gida da misalin karfe 6 na yamma, lokacin da ba mu gansu ba, sai muka buga waya ga ’yan uwa da ke Kano, inda suka ce mana sun hau motar bas zuwa Zariya.

“Nan nayi ta buga waya, kafin daga bisani aka gaya min hatsarin a kan hanyarsu, don haka na zo kuma duk da konewar da suka yi, na iya gano gawarwakinsu,” in ji shi.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *