Masu garkuwa sun sace ɗalibar UDUTH a hanyar Sokoto zuwa Shinkafi

0
458

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wata ɗalibar Makarantar koyon aikin jinya da ungozoma da ke Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usman Danfodiyo (UDUTH) Sokoto.

An tattaro cewa wacce aka kama mai suna Zahra Umar, an yi garkuwa da ita ne a hanyar Sokoto zuwa Shinkafi a ranar Asabar, 30 ga Yuli, 2022. 


Wani ma’abucin Facebook, Abdul-Rahman Geto, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin, 1 ga watan Agusta, ya ce masu garkuwa da mutanen sun tuntuɓi iyalanta inda suka buƙaci a biya su N30m kudin fansa amma daga baya sun mayar da shi zuwa miliyan uku bayan tattaunawa. 

Ya ruwaito cewa:
“Yan bindiga sun sace wannan yarinya zahra a hanyar Sokoto zuwa Shinkafi ranar Asabar, daliba ce a UDUTH sokoto, a ranar Asabar din da ta gabata ne suka nemi kudin fansa Naira miliyan 30, amma a jiya bayan sun dauki tsawon lokaci suna tattaunawa sun mauar da kudin Naira miliyan 3, ina rokon Allah Ya sa ta dace, ta dawo da ‘yancinta da wuri-wuri.” ya rubuta.

Leave a Reply