Masu garkuwa sun kashe ɗan bautar ƙasa, bayan karɓar kuɗin fansa

Wasu ‘yan bindiga waɗanda ake kyautata zaton cewa masu garkuwa ne, sun kashe wani ɗalibi mai suna Abdulmalik Tukur, da ya kamala karatunsa a jami’ar Modibbo Adama (MAU), da ke Yola jihar Adamawa bayan sun karɓi kudin fansa naira dubu dari biyar.

Majiyarmu wadda ke kusa da iyalin ta bayyana mana, mamacin bai daɗe da kamala bautar ƙasa ba a bana, masu garkuwa sun tafi da shi tare da wasu mutane.

Ɗalibin mai kimanin shekara 32, kwanan nan ya kamamla bautar ƙasa a jihar Filato, a kan hanyarsa ta dawo wa gida, masu garkuwan suka kama shi tare da wasu mutum shida.
Dukkan wadanda aka kama su tare, an sake su bayan sun biya kuɗin fansa naira dubu ɗari hudu kowannensu, amma shi Tukur sai suka ce, sai an kawo naira dubu ɗari biyar.

Bayan an daɗe ana tattauna wa, sai suka daidaita akan za a ba su naira dubu ɗari biyar, a matsayin kuɗin fansa.Ya ce, an ɗauki kuɗin an kai wa masu garkuwar a daji.

Bayan sun karɓi kudin sun nuna musu wanda suka yi garkuwar da shi, sai suka miƙa musu, suka ce, ga shi nan su tafi da shi, ba yan sun juya za su tafi, sai suka harbe shi da bindiga, nan take ya fadi ya mutu.

Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar Adamawa SP Sulaiman Nguroje, har zuwa lokacin hada wannan labari, ya ce, bai samu wani bayani a kan wannan labari ba.


Comments

3 responses to “Masu garkuwa sun kashe ɗan bautar ƙasa, bayan karɓar kuɗin fansa”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Masu garkuwa sun kashe ɗan bautar ƙasa, bayan karɓar kuɗin fansa […]

  2. […] KU KUMA KARANTA: Masu garkuwa sun kashe ɗan bautar ƙasa, bayan karɓar kuɗin fansa […]

  3. […] KU KUMA KARANTA: Masu garkuwa sun kashe ɗan bautar ƙasa, bayan karɓar kuɗin fansa […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *