Manyan shugabanni, haziƙai ‘yan asalin Borno

0
406

Jihar Borno ita ce zuciyar yankin Arewa maso Gabashin Najeriya kafin zuwan ƙungiyar Boko Haram a shekarar 2009.

Borno ta yi suna wajen samar da manyan shugabanni, masana a ciki da wajen Najeriya. Ɗan Najeriya na farko da ya samu mukaymin Kyaftin a Sojan Burtaniya (1953) bayan ya yi rawar gani a yakin duniya na ɗaya da na biyu shi ne Cpt Kyari Magumeri.

Babban Sajan na farko (RSM) na Kwalejin Tsaro ta Najeriya (1964) shi ne Manjo Bulama Biu.

Gwamnan yankin Arewa na farko (a lokacin shi ne jihohi 19 daga 1962 zuwa 66) marigayi Sir Kashim Ibrahim, Sufeto Janar na ‘yan sanda na farko daga Arewacin Najeriya, kuma IGP ɗaya tilo da ya yi aiki na tsawon shekaru 9 a Najeriya (1966-1975) shi ne IGP Kam-selem.

Ministan Man Fetur na farko a Najeriya (1972) shi ne Shettima Ali Monguno (PhD).

Minista na farko na gwamnatin farar hula a Najeriya da ya rattaba hannu tare da miƙa mulki ga sojoji (bayan juyin mulkin 1966) marigayi Zanna Bukar Dipcharima, shi ne ministan ayyuka na farko a Najeriya (1957) sannan ya naɗa Tafawa Balewa.

Ɗan Najeriya na farko da aka naɗa a matsayin babban kwamandan runduna ta daya ta sojojin Najeriya (1967) shi ne Janar Mamman Shuwa. Bature na farko da ya samu horo a Makarantar Soja ta Sandhurst, sannan kuma wanda ya fara horas da sojoji na farko a Sojojin Najeriya shi ne Birgediya Janar Zakaria Maimalari.

Baƙar fata na farko da ya fara watsa shirye-shirye a kafar BBC Landon shi ne Ambasada Abba Zoru.

Mace ta farko data fara wallafa littatafai na Turanci daga Arewacin Najeriya take, Farfesa Zainab Alkali.

Farfesan farko daga Arewacin Najeriya Umaru Shehu (Shi ne HOD na farko, Sashen kula da magungunan al’umma na jami’ar ABU Zaria; tsohon mataimakin shugaban jami’ar Najeriya Nsukka; tsohon shugaban jami’ar Maiduguri tilo; tsohon Pro- Chancellor kuma shugaban majalisar gudanarwa na Jami’ar Bayero Kano da Jami’ar Legas, Farfesa Emeritus, Kiwon Lafiyar Jama’a, Jami’ar Maiduguri, tsohon shugaban Kwalejin Kimiyya ta Najeriya kuma tsohon shugaban kasa, makarantun likitanci a Afirka).

Leave a Reply