Maniyyatan jihar Kaduna za su biya kuɗin kujerar hajji cikin wata biyu

0
196

Manniyyatan aikin Hajji daga Jihar Kaduna za su biya kafin-alƙalamin Naira miliyan biyu da dubu ɗari biyar, sannan su biya cikon miliyan biyu kafin ƙarshen watan Disamba.

Hukumar jin daɗin alhazai ta jihar Kaduna ta ba wa maniyyatanta wa’adin ranar 30 ga watan Disamba 2023 su kammala biyan cikon kuɗin kujerar aikin Hajji mai zuwa.

Hukumar ta umarci maniyyatan su biya Naira miliyan 2.5 a matsayin kafin alƙalami, sannan su biya cikon Naira miliyan biyu kafin cikar wa’adin.

Ta bayyana cewa za ta ba da fifiko da maniyyatan da ba su taɓa sauke farali ba wajen yin rajista, amma ba za ta amince da biyan kuɗin kujerar a bisa wakilci ba.

KU KUMA KARANTA: Maniyyata aikin Hajjin 2024 za su biya miliyan huɗu da rabi – NAHCON

Duk wanda aka maye gurbinsa a kujerar aikin Hajjin da ya biya kuma, to ba za a dawo masa da kuɗinsa ba, sai an kammala dawo da alhazai daga ƙasa Mai Tsarki.

Ta ce ɗaukar matakin ya zama dole saboda yadda wasu ke biyan kuɗin kujerar ba da niyyar su tafi ba, sai don daga baya su sayar wa waɗanda ba su samu ba da tsananin tsada.

Hukumar ta ce duk wanda ta gano ya yi haka to ba za ta amince ta maye gurbinsa ba, inda ta garagaɗi maniyyata su guji biyan kuɗi ta hannun jami’anta, su biya kai tsaye a banki sannan su kai takardar shaidar biyan kudinsu ga jami’an Hajji da ke kula da ƙananan hukumominsu.

Hukumar Aikin Hajji ta ƙasa (NAHCON) ta sanya Naira miliyan 4.5 a matsayin kuɗin kujerar aikin Hajjin na 2024.

Leave a Reply