Man United ba za ta sayo Bellingham na Real Madrid ba

0
118

Attajirin nan da ke cikin mamallakan ƙungiyar Manchester United, Jim Ratcliffe, ya bayyana cewa ba zai nemi ƙungiyar ta sayo gwanayen ‘yan wasa irinsu Jude Bellingham, ɗan asalin Ingila wanda ke buga wasa a Real Madrid ba.

Ratliffe yana yunƙurin farfaɗo da tagomashin Man United ne, inda ya ce burinsa shi ne kawar da Manchester City da Liverpool daga jagorancin gasar Firimiya.

A kwanakin baya ne Ratcliffe, attajirin ƙasar Ingila ya karɓi ragamar mallakar ƙungiyar bayan ya saka Fam biliyan £1 (Dala biliyan $1.2) ya sayi kashi 25% na hannun jarinta.

Yayin da kocin ƙungiyar Erik Ten Hag yake shekara ta biyu a matsayin manajan Man United, ana sa ran za su saka maƙudan kuɗi don sayan ‘yan wasa masu tsada a ƙarshen kakar bana.

KU KUMA KARANTA: Ba za a manta da Pele ba, in ji hukumar kwallon kafa ta FIFA

Rabon da Man United ta ci kofin Firimiya tun 2013, kuma a kakar bana ma suna mataki na shida ne a teburin na Firimiya, duk da dai sun kai matakin kusa da na ƙarshe a gasar FA, bayan doke Liverpool ranar Lahadi.

Yayin da Ratcliffe, wanda yake da shekaru 71 a duniya, ya fito a shirin ‘Cycling Club podcast da Geraint Thomas ke gabatarwa, an tambaye shi ko zai nemi sayan ɗan wasan tsakiya na Ingila Bellingham daga Real Madrid.

Ratcliffe ya ce, “Bellingham babban ɗan wasa ne, amma ba ya gabanmu. Mafitar da muke nema ba ta kashe maƙudan kuɗi kan sayo manyan ‘yan wasa ba ce”.

“An gwada haka a baya, idan ka duba shekaru 10 da suka wuce. An kashe tarin kuɗaɗe kan wasu tsirarun ‘yan wasa.

“Abu na farko da ya kamata mu yi shi ne mu nemo ‘yan wasan da suka dace a wajen da ya dace don gudanar da ƙungiyar. Kuma za mu tabbatar da mun ɗauko su, wannan shi ya fi dacewa da abin da ke faruwa a duniyar ƙwallo ta yau.”

A cikin shirin, an tambayi Ratcliffe idan zai zaɓi tsakanin sayo Kylian Mbappe na Faransa ga Man United, ko ɗan tseren keke Tadej Pogacar ga kulob ɗinsa na tsere na INEOS.

Ya ce, “Gara a ce na sayo wanda a nan-gaba zai riƙa ya zama kamar Mbappe, maimakon na zuba maƙudan kuɗi wajen sayen Mbappe na yanzu”.

Rahotanni sun nuna cewa Mbappe ya amince ya koma ƙungiyar Real Madrid daga Paris Saint-Germain a ƙarshen kakar bana.

Kuma ko da Mbappe yana kasuwa a yanzu, shahararren ɗan wasan ba zai iya cika buƙatun Ratcliffe ba.

Ratcliffe ya ƙara da cewa, “Sayan Mbappe ba wani abin birgewa ba ne. Kowa zai iya gane haka. Babban ƙalubalen shi ne nemo wanda zai iya zama tamkar Mbappe ko Bellingham ko Roy Keane a nan-gaba”.

Leave a Reply