Majalisar Koli Ta Najeriya Ta Yiwa Dariye, Nyame Da Wasu Mutane 157 Afuwa

Daga; Rabo Haladu.

MAJALISAR Koli ta Najeriya wadda ta kunshi tsoffin shugabannin kasa da tsoffin manyan alkalai da shugaban kasa mai ci da gwamnonin Jihohi ta amince da shirin afuwa ga mutane 159 da kotuna suka samu da aikata laifuffuka daban-daban cikin su harda tsohon Gwamnan Jihar Filato Joshua Chibi Dariye da takwaransa na Taraba Jolly Nyame.

Ministan shari’a na kasa, Abubakar Malami ya shaidawa manema labarai daukar matakin bayan taron da Majalisar ta gudanar a karkashin shugabancin shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya kuma samu halartar tsoffin shugabannin kasar da suka hada da Janar Yakubu Gowon, Janar Abdusalami Abubakar, Goodluck Jonathan da shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan da wasu ministoci.

Malami ya ce daukar matakin ya biyo bayan shawarar da kwamitin dake nazari da gabatar da bukatar yiwa wadanda suka aikata laifuffukan kuma suka kwashe wani lokaci na hukuncin da aka yanke musu a gidan kaso.

Ministan yace kwamitin ya bada shawarar yiwa mutane 162 afuwa, kuma Majalisar ta amince da bukatar a kan mutane 159, inda taki amincewa da na mutane 3, cikin su harda wani tsohon manajan bankin da ya wawure naira biliyan 125 kudin jama’a, wanda kotu ta daure shekaru 120 a gidan


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *