Mahimmanci da tsarin tsaftace firiji a ko wane lokaci

Yadda tsabtar firijin (na’urar tsaftace abinci) ku ya ke, shi yake ƙara tabbatar da tsaftar ku, wanda hakan ke nuna yanayin lafiyarku da ta iyalanku.

Dattin firiji na iya zama wurin taruwar ƙwayoyin cuta kamar salmonella, E. coli da listeria da sauran ƙwayoyin cuta.

Firiji mai tsabta zai bai wa jikinku ƙarfin amfana daga abincin kuke ci daga cikinsa, kuma zai rage haɗarin cututtukan da ke da alaƙa da abincin da aka saka cikin firiji. Haka kuma tsaftace shi, tare da cire duk abubuwan da ke maƙalewa a jiki zai taimaka wajen samar da ƙarin sarari da inganci, da kuma zagayawar iska a cikinsa.

Firiji mai tsabta da tsari zai iya inganta jituwar gida.

Firiji mai datti da ɗauɗa na iya zama ɓoyayyen tushen damuwa ga dukan iyali.

Damar Samun abin da kuke nema da sauri zai iya kare ku daga ɓata lokaci, ya kuma ya rage yawan damuwa.

KU KUMA KARANTA:Amfanin Alobera (ALOE VERA) ga ɗan Adam

Firiji mai tsafta da tsari zai sa ku zama masu iyayin girki, kuna iya tsarawa, dafawa da cin abinci mafi koshin lafiya lokacin da kuke da cikakkiyar ra’ayi na kayan abinci da kuke da su.

Har ila yau, sanin ainihin abin da kuke da shi a cikin firiji yana ba ku damar haɗa kayan abinci don ba da girke-girke mai daɗi, a matsayin ƙari.

Yayin aiwatar da tsaftace firijin ku, kuna iya cin karo da wasu abubuwa da basu ɓaci ba, waɗanda zaku iya amfani da su cikin abin da za a dafa a gaba.

Abubuwan da ake buƙata don tsaftace firijin sun haɗa da: ruwan zafi, kunfar sabulu; tawul mai tsabta; ruwa mai tsafta.

Mataki 1 – Tsaftace firijinku : Ku cire dauɗa da duk abubuwan datti da ke cikin ku sanya su akan tebur, yayin da kuke tsaftace shi.

Fitar da duk wasu sassa masu cirewa.

Kada ku bar abinci har ya kai sa’o’i 2 ba a cikin firiji ba.

Mataki na 2 – Wanke duk wasu sassa masu cirewa da hannu da ruwan zafi,da sabulu mai kunfa.
A busar da tawul mai tsabta.

Kada kuyi anfani da ruwan zafi dan wanke sassan gilashin mai sanyi, saboda gilashin zai iya tsagewa.

Barin su a wuri me dama dama.

Mataki na 3- Tsaftace cikin firiji

Goge cikin firinjin in da ba komai a ciki da ruwan ɗumi, ruwan sabulu; sannan a watsa ruwa,dan kunfan ya tafi.

A goge da tawul mai tsabta.

Kar ku manta da goge cikin kofofin da duk wani wajen da ba za a iya cirewa ba.

Mataki na 4 – Mayar da duk sassan da aka cire, da abincin da aka cire.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *