Mahara sun ƙona gidaje goma a ƙaramar hukumar Rogo ta Jihar Kano

Daga Shafaatu DAUDA, Kano

Wasu mahara sun kai farmaki ga al’ummar Dan Jamfari dake ƙauyen Barbaji a ƙaramar hukumar Rogo ta jihar Kano tare da ƙona gidaje 10.

Sakataren zartarwa na hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kano, Alhaji Saleh Jili, ya bayyana a ranar Juma’ar nan cewa hukumar ta jajantawa waɗanda abin ya shafa tare da kai musu kayan agaji.

Ya ce gwamnatin jiha ba za ta bar wannan abu yatafi a banzaba Dole sai ta kamo wadan da suka Aikata Wannan Abu domin gurfanar Dasu agaban Kuliya.

Kayayyakin agaji da aka baiwa waɗanda abin ya shafa sun haɗa da bandir ɗin kwanon rufi guda 10, buhunan siminti 20, fakiti 10 na ƙusoshi, buhunan shinkafa mai nauyin kilogiram 10, guda 20, masara 20 da gishiri buhu biyar.

Wadanda ya abin ya shafa sun kuma samu kayan sawa, bokiti, dama kayan lambu da kwali biyar na kayan magi.

Jili ya jaddada ƙudurin gwamnatin jihar kano na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan jihar sannan ya buƙaci mazauna yankin da su zauna lafiya da juna.

Wani mazaunin garin, Malam Magaji Audu, ya ce maharan na ɗauke da sanduna da katakwaye.

“Fiye da mutane 200 daga cikinsu ne suka mamaye kauyen cikin dare suna bi gida-gida suna neman babur dinsu da suka sace.

“Maharan sun yi ƙoƙarin daɓa min wuka a gaban ‘yan uwana kuma na ƙi fitar da ‘ya’yana wadanda suka ce sun sace babur ɗinsu kamar yadda suka bukata,” inji shi.

Audu ya bayyana cewa washegari ne maharan suka dawo inda suka banka wa gidansa da sauran mutane wuta yayin da ‘yan uwansa suka tsere.

Yan bindigar sun kwashe kayan abinci, kaji, mai, kayan aikin noma tare da lalata gidaje 10 a kauyen,” in ji shi.

Hakimin Rogo, Alhaji Muhammad Maharazu, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma yabawa hukumar bayar da agajin gaggawa bisa irin wannan kayay yakin da suka bayar


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *