Mahaifiyar matar da mijinta ya kashe akan biredi ta buƙaci adalci

Cordelia Anene, mahaifiyar marigayiya Ogochukwu Anene, wadda ake zargin mijinta, Wilson Uwaechina, ya kashe ta a kan biredi, ta buƙaci a yi ma ‘yar ta adalci.

Marigayiyar, ‘yar asalin ƙauyen Umuokpu, Awka, jihar Anambra, ta auri Uwaechina, wanda ya fito daga jihar Enugu. Ana zargin ya kashe ta ne a wani rikici da suka yi a kan biredi.

KU KUMA KARANTA: Yadda wani mutum ya kashe matar sa saboda burodi

Cordelia ta buƙaci a yi mata adalci a lokacin da ta ziyarci kwamishiniyar mata da walwalar jama’a ta jihar Anambra, Ify Obinabo, a ofishinta a ranar Talata.

A yayin da take zargin mijin ne ya kashe ‘yarta, matar ta bayyana cewa marigayiyar Ogochukwu ta sha dukan tsiya daga mijin ne bayan ya cinye burodin data sayawa yara, kuma da yaran suka nuna suna son biredin sai mijin ya fusata harda tambayar dalilin da ya sa zasu tuhumeshi game da burodin. Ta ce hakan ne ya sa mijin ya riƙa dukan matar tasa da madubi da wasu abubuwa, wanda hakan ya sa ta fita hayyacinta.

Misis Anene ta bayyana cewa, kwanaki kaɗan bayan da ya yi mata dukan, an kwantar da ɗiyarta a asibitin Neja Foundation da ke Enugu, inda ta yi ta zubar da jini a ciki sakamakon raunukan da ta samu a lokacin da aka yi mata duka.

Ta ce, “Likitocin sun tabbatar da hakan ne bayan wani bincike da aka yi mata, inda suka tura mu asibitin koyarwa na jami’ar jihar Enugu da ke Ituku Ozalla.”

Ta koka da cewa yayin da duk waɗannan ke faruwa, ba a ga wanda ake zargin ba.

Mahaifiyar me rasuwar ta ce maimakon su nemi rahoton abinda ya kashe ta, ɗan sandan da ke kula da lamarin a Enugu ya roƙe su da su janye ƙarar.

Ta yi kira ga gwamnatin jihar Anambra da ta taimaka mata a yiwa ɗiyarta adalci.

Da yake mayar da martani, kwamishiniyar matar Obinabo, ta ce, “a halin yanzu ana ci gaba da bincike don gano ainihin musabbabin mutuwar marigayiya Ogochukwu Anene.”

Ta kuma buƙaci matan da ke cikin auratayya da su riƙa faɗa idan akwai matsala ta cin zarafi a aurensu, su kuma dinga neman taimako.


Comments

One response to “Mahaifiyar matar da mijinta ya kashe akan biredi ta buƙaci adalci”

  1. […] KU KUMA KARANTA:Mahaifiyar matar da mijinta ya kashe akan biredi ta buƙaci adalci […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *