Lauyoyin hamɓararren shugaban Jamhuriyar Nijar, Mohammed Bazoum sun buƙaci kotun Ecowas da ta umurci a mayar da shi kan mulki kasancewar hamɓarar da shi da aka yi da kuma tsare shi sun saɓa wa doka.
Alfijir Labarai ta rawaito an tsare da Bazoum ne tun bayan da sojoji masu gadin fadar shugaban ƙasar suka hamɓarar da shi daga mulki ranar 26 ga watan Yulin 2023.
Sojojin sun zargi gwamnatin Bazoum da gaza magance matsalar tsaron ƙasar.
Sai dai ɗaya daga cikin lauyoyinsa waɗanda suka garzaya kotun Ecowas, Seydou Diagne, a bayanin da ya yi, ya buƙaci kotun, wadda ke zaman ta a Najeriya ta yanke hukunci cewar “hamɓarar da shi da aka yi ƙarfi da yaji take hakkinsa ne na shiga harkokin siyasa.”
Kotun Ecowas, kotu ce wadda kan yanke hukunci kan ƙararraki daga ƙasashen yammacin nahiyar Afirka, sai dai ba wajibi ne ga ƙasashe su yi amfani da hukuncin kotun ba kasancewar babu takamaiman tsarin tabbatar da hukuncin.