Connect with us

Gani ga Wane

Labari cikin hotuna: Yadda Kiristoci suka taya Musulmi gyaran filin Sallar Idi

Published

on

Aikin gyaran filin idi

Wannan abu ya faru ne a Kudancin Kaduna, inda kiristoci suka fito domin taya musulmai gyara filin da za ayi sallar idi. Sunyi hakan ne, a matsayin wani bangare na shirye-shiryen Babbar Sallah, da kuma ƙarfafa zaman tare.

1 Comment

1 Comment

  1. Pingback: Kiristoci sun taya musulmi gyaran masallacin Idi a Kachia | Neptune Prime Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Al'ajabi

Yadda aka horar da ɓeraye wajen ceto mutane yayin girgizar ƙasa

Published

on

Kampanin Apopo na ƙasar Belgium ya horar da wasu haziƙan ɓeraye domin yin aikin ceto ga waɗanda ɓaraguzan girgizar ƙasa suka danne har yau ba a gano su ba.

“Anyi amfani da ɓeraye ne saboda a yanayin tsarin halittar su, suna da sha’awar sanin abu, da kuma son kutsa kai da bincike, wannan dalili yasa aka gane tsaf zasu iya taimakawa wajen ceto,” in ji Donna Kean, ƙwararren masanin kimiyyar ɗabi’a kuma shugaba mai jagorarantar aikin.

Masu bincike na APOPO yayin horarwa

“Banda ɗabi’ar ɓera na binkice da shige shige, ƙanƙantar halittar su, da baiwar jin ƙamshin da wari koda daga nesa, ya beraye suka zama mafi chanchanta don yiwa duniya wannan aiki”, in ji Kean.

KU KUMA KARANTA: Allah ɗaya gari bam bam! Gizo-Gizo, abincin yau da kullum a Kambodiya

An sanyawa ɓerayen wata babbar jaka da take ɗauke da na’urar GPS ta zamani da kyamarar ɗaukar hoto mai inganci, da kuma makirufon.

Haka kuma akwai wata na’urar wayar salula da za a iya magana da mutanen da suka maƙale amma ba su kai ga rasa rayukansu ba.

Yayinda akema ɓerayen gwaji

Sannan za a iya ganin mutumin da abin ya rutsa da shi, gami da gane irin yanayin da yake ciki, sannan a gano hanya mafi sauƙi da za a iya ceto shi a fito da shi.

Wannan ya zama izina garemu mutane, idan har ɓera yana kishin ƙasarsa, yana bada gudunmawa mai mahimmanci wajen cigaban ƙasa, ya kamata mu tambayi kanmu, mu wane gudunmawa muke bawa ƙasar mu domin cigaban ta, a matsayin mu na yan Adam.

Continue Reading

Gani ga Wane

Kotu ta umurci budurwa ta biya saurayinta N150,000 bayan ta karɓi kuɗin mota N3000 ta kuma ƙi amsa gayyatarsa

Published

on

Kotu ta umarci wata mata da ta karɓi naira dubu uku kuɗin mota wajen saurayinta domim ta ziyarce shi, amma daga baya ta kashe wayarta, ta ƙi zuwa, da ta biya saurayin kuɗi naira dubu N150,000, bayan da saurayin ya kai ƙarar budurwa tasa kotun.

Kotun da ke zama a jihar Enugu ta yanke hukuncin ne dan koya wa mata masu yaudara darasi, domin shari’ar ta zamo izina ga wasu matan.

KU KUMA KARANTA:Yadda wani mutum shaƙe budurwarsa saboda cin amana, ya kuma cinna wa kansu wuta

Wani Lauyan Najeriya mai suna @Egi_nupe_ a shafinsa na tweeter, ya bayyana hakan a shafin Twitter, ya ce matar ta kashe wayarta bayan ta karɓi kuɗin kuma hakan ya fusata saurayin nata.

Mutumin da bai ji daɗin abin da ya faru ba, ya garzaya kotun shari’ar Enugu inda ya yi nasara.

A cikin hukuncin, alkalin kotun ya ce abin da matar ta aikata yaudara ne.

Adadin tarar da aka ɗora wa matar, an yi ne don ya zama izina ga sauran mata masu irin wannan dabi’a ko tsare-tsare na yaudara.

Continue Reading

'Yansanda

Yadda aka tsinci gawar ma’aurta a kan gadon aurensu a Kano

Published

on

A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne aka tsinci gawar wani magidanci mai suna Sulaiman Idris mai shekaru 28 tare da gawar matarsa ​​Maimuna Halliru mai shekaru 20 a kan gadon aurensu.

A wata sanarwar da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kano, SP Haruna Kiyawa ya fitar, ya ce ma’auratan ba su fito daga gidansu ba, tun ranar Laraba 02/01/2023, inda suka shafe kimanin awa 23 a ɗaki.

Ya ce “A ranar Litinin, 03/01/2023 da misalin ƙarfe tara na safe, an samu rahoto daga ƙauyen Kwa, na ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, a jihar Kano cewa wasu ma’aurata, Sulaiman Idris, da matarsa Maimuna Halliru, ba su fito daga gidansu ba tun ranar 02/01/2023 da misalin ƙarfe 11:00 na dare.

Binciken farko, an gano cewa ma’auratan da suka mutu sun kunna wuta don dumama ɗakinsu saboda sanyin da su ke ji, kuma ko’ina a kulle, dalilin haka hayaƙi ya balbale su a lokacin da suke barci.

“Lokacin da kakar mijin buɗe ƙofar ɗakinsu da ƙarfi, sai ta tarar da ma’auratan basa motsi a kan gadon su, ta kuma iske da ragowar hayaƙi a ɗakin.

“Bayan samun rahoton, kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Mamman Dauda, ​ya umurci tawagar ‘yan sanda ƙarƙashin jagorancin CSP Ahmed Hamza,DPO na ‘yan sandan reshen Dawakin Tofa da suje suga wurin, inda suka ka kai ma’auratan asibitin ƙwararru na Murtala Mohammed da ke Kano kuma a nan wani likita ya tabbatar da mutuwarsu.

Kwamishinan ‘yan sandan ya shawarci al’ummar jihar Kano da su yi taka-tsan-tsan wajen amfani da wuta, da kuma lantarki, sannan a kula da ɗaukar matakan kariya saboda lokacin sanyi yana da alaƙa da haɗarin gobara.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like