Kwalliyar bikin Sallah ga mata

0
126

Assalamu alaikum ’yan uwana mata. Kasancewar an fara bukukuwan Babbar Sallah ya sa na yi wannan rubutu domin taimaka wa waɗanda za su caba kwalliya da Sallar.

Saboda yadda masu sana’ar kwalliyar fuska suke cika kuɗi, yana da kyau mata su koyi yadda za su yi kwalliya da kansu, ba tare da sun kashe ko sisi ba, kuma yadda ko da bayan Sallar za su iya yin irin wannan kwalliya domin burge mazansu a kullum.

Ya kamata fitar da za a yi a bikin Sallah ta fi ta koyaushe kyau.

Kayan kwalliyar da ake bukata:

Gazal launin baki da mai ruwan kasa

‘Eye shadow’

Hoda

‘Mascara’

Jan jambaki ( shi ne ake yayi yanzu)

Fandesho (foundation)

Hodar ‘Blush’

Ma’askar gira (tweezers) ka’idoji

Kafin a fara komai, za a wanke fuska da sabulu mara karfi.

A dauko ma’askar gira (tweezer) ki sa a saman girar ki yi tsari mai kyau.

Sai a jira fuskar ta bushe. Bayan fuskar ta bushe, sai a shafa mai kadan a fuskar musamman in fatar mai gausti ce. In ko mai laushi ce, to ba sai kin shafa mai ba.

A shafa hodar fandesho mai launin fata. Sannan a bar ta kamar minti uku. Sai a samu hoda mai kama da launin fatar a shafa a fuska har wuya Kwalliyar bikin Sallah da kunnuwa. Saboda kada launin fuskarki ya bambanta da na wuya.

A samu gazal musamman ma launin ruwan ƙasa (dark brown) sai a zana a girar da aka aske.

“Eye shadow” launin kayan da za ki sa sai a shafa kamar launi biyu a kan fatar idon.

Kwalli: A shafa a ido sannan maskara (mascara) launin shuɗi (blue) ko baki a gashin ido, ana taje shi.

Hodar ‘blush’: A shafa ita ma daidai da launin fatar fuska.

Jambaki: A shafa a lebba. Bayan an yi hakan, sai a sake samun gazal mai launin kasa a bi leɓɓan bakin da shi. Bayan an gama waɗannan abubuwa, za a ga fuskar ta canza sosai.

Leave a Reply