Kungiyar Mata Ta Wopin Ta Yi Kira Ga Gwamnati, Kungiyoyi Game Da Zaman Lafiya

0
291

Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.

KUNGIYAR Mata masu fadakarwa a samu zaman lafiya a kowane irin mataki mai suna “Women For Peace In Nigeria” ta yi kira ga Gwamnati, da daukacin kungiyoyi da su kara zage damtse domin tabbatar da zaman lafiya a dukkan sako da lungun kasar baki daya.

Shugabar kungiyar (WOPIN) ta kasa reshen Jihar Kaduna uwargida Grace Magaji, ta yi wannan kiran ne a wajen babban taron lacca na shekara-shekara da aka yi wa taken gudunmawar kafafen yada labarai wajen kokarin gina kasa da ci gabanta domin amfanin jama’a baki daya.

Kamar yadda ta ce a lokacin da take gabatar da jawabi a wajen taron zaman lafiya na taka mihimmiyar rawa wajen ci gaba da kuma gina ta baki daya.

“idan babu zaman lafiya ba za a samu wani abu mai ma’ana ba wajen ciyar da al’umma gaba”, inji ta.”

Wannan dalili ne ya sa muke kara jaddada yin kira ga Gwamnati da dukkan kungiyoyi masu zaman kansu, kama daga na kokarin kare hakkin bil’adama da sauran makamantansu da su ci gaba da kokarin samar da zaman lafiya a tsakanin jama’a.

Saboda da haka muke kara fadakar da jama’a su ci gaba da fadakarwa a tsakanin jama’a, a Jihar Kaduna da kasa baki daya.

Da yake gabatar da jawabinsa masanin al’amuran yau da kullum shugaban al’umma Alhaji Hassan Sardaunan Hayin Banki Kaduna kira ya kara yi ga yan jarida da sauran kafafen yada labarai da su kara himma wajen fadakarwa ga jama’a domin samun zaman lafiya a tsakanin al’ummar kasa.

Sardauna ya ci gaba da cewa ya na daga cikin abubuwan da za su samar da ci gaba da zaman lafiya jama’a su kara himma wajen zaben mutanen da za su rike amanar dukiyarsu da tabbatar da zaman lafiya.Ya ce babban al’amari da yake taka muhimmiyar rawa wajen samar da zaman lafiya shi ne kowa ya tashi tsaye a samu abin yi da za a dogara da shi.

An samu halartar dimbin jama’a daga bangaren kungiyoyi masu zaman kansu,da masu fafutukar kare hakkin bil’adama da kuma wakilai daga kafafen yada labarai na Rediyo,Talbijin, Jaridu da kuma kafafen yada labarai na yanar Gizo, kuma dukkan mahalarta taron sun bayyana gamsuwarsu da irin yadda taron na Bana ya kasance da kowa ya rika bayyana farin cikinsa da taron kokarin fadakarwa domin samar da zaman lafiya.

Leave a Reply