Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.
WANI dan takarar shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar PDP, Mista Peter Obi, ya bayyana cewa kasar Najeriya na da duk abin da ake bukata domin ta zama babbar kasa amma rashin shugabanci nagari ya sanya duk ta sukurkuce.
Tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, ya bayyana hakan ne a Kaduna ranar Litinin yayin Da yake jawabi ga wakilan Jam’iyyar PDP masu zaben fidda gwanin da aka shirya gudanarwa a Abuja a cikin wannan wata, inda ya ce shi kadai ne dan takararsa da zai iya magance matsalar Najeriya.
Ya kara da cewa, ya lura da takaicin cewa gazawar jagoranci na miyagu a cikin shekaru ya haifar da masifun da Najeriya ta jefa al’ummarta cikin talauci fiye da kowace kasa.
Ya ce “Abin da muke yi yanzu shi ne raba kudin man fetur da jefa mutane cikin talauci da sauran matsaloli da suka hada da rashin aikin yi, rashin tsaro gami da yunwa.
“Sama da kashi 80% na yawan noma, manoma a Kaduna ba za su iya zuwa gona ba saboda rashin tsaro. Muna da matalauta da yawa a duniya fiye da Indiya da China. Dole ne mu yi wani abu ko kuma, al’amura za su yi muni,” in ji shi.
Obi wanda ya yi dogon bayani kan rashin tsaro ya ce babu tsaron da za a je wani yanki na kasar nan, musamman Kaduna inda hatta kamfanonin jiragen sama ke kin zuwa.
Acewarsa, makamashi da gogewarsa a matsayinsa na dan kasuwa da kuma tsohon dalibin jami’o’in Cambridge da Oxford da kuma makarantar kasuwanci ta Landan, idan aka zabe shi, zai ceto Najeriya daga durkushewa.
Ya ce “makomar ‘ya’yanmu tana hannunmu, akwai bukatar mu sanya makomar yara a gaba ba kudi ba”.
Don haka ya bukaci wakilan da su zabi ‘yan Najeriya masu nagarta da za su iya gyara kasar nan.
Dan takarar shugaban kasa ya kuma yi alkawarin kara saka hannun jari a harkar bunkasa matasa.
Masanin Tattalin Arziki ya koka da yadda gwamnatin APC ta karbo rancen naira tiriliyan hamsin da takwas kuma ‘yan Najeriya na fama da talauci, inji shi.
Ya kuma tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa shi ne dan takara daya tilo da zai iya gyara Najeriya, yana mai cewa akwai bukatar Najeriya ta saka hannun jari a makomar ‘ya’yanmu, in ji shi.
A nashi jawabin, Shugaban Jam’iyyar PDP Jihar Kaduna, Honarabul Hassan Hyet, ya bayyana Jindadinsu bisa ziyarar da dan takarar, kana ya bayyana cewa zasu zauna domin yin shawarar da ta dace na ganin cewa sun yi abin da ya dace.
Acewarsa, mafi akasarinsu basu da masaniya a kan irin halin da kasar ke ciki, amma kasancewar shi kwararre kuma masani ya wayar musu da kai, don haka dole su yi takatsantsan wajen zaben wanda ya kamata su tsayar a matsayin dan takarar Jam’iyyar.
A karshe, Shugaban Honarabul Hassan Hyet, ya taya dan takarar fatan alheri bisa kudirinsa na tsayawa takara a karkashin Jam’iyyar, kana ya masa addu’ar samun nasara.