Daga Fatima GIMBA, Abuja
Kotu ta yankewa wani matashin me koyon aiki, mai suna Nwankwo Ifeanyi hukuncin ɗaurin rai da rai bayan an same shi da laifin yin lalata da wata yarinya ‘yar shekara huɗu a Legas.
Ifeanyi ya kasance yana koyan aiki gurin ubangidan nasa har sai sanda a yanke masa hukumcin, kuma an tattaro cewa ya aikata laifin ne a gidansu, a watan Yunin 2017, kamar yadda lawandevents.com ta ruwaito.
Daga baya aka kama shi aka gurfanar da shi a gaban kotu.
Da yake karanta tuhume-tuhumen, Mai shari’a R. A. Oshodi na kotun laifuffuka na musamman da ke Ikeja, Jihar Legas, ya ce: “Kai Nwankwo Ifeanyi, a ranar 20 ga watan Yuni, 2017, a lamba 11, Joy Street, Ojo, ka yi lalata da yar shekara huɗu, ta hanyar sanya yatsu cikin al’aurarta.”
Domin tabbatar da laifin da ake tuhumar wanda ake tuhuma (Ifeanyi), shaidu biyu sun ba da shaida ga masu gabatar da ƙara, yayin da kuma wanda ake tuhuma ya gabatar da shaidu biyu, ciki har da ɗan uwan wanda ake ƙara, Nwankwo Nnamdi.
Alkalin ya ce, “Mahaifin yarinyar ya kasance mai sana’ar da na’urorin lantarki ne, yayin da wanda ake tuhuma shi yaronsa ne wanda ke zaune a gida ɗaya da su.
“Wanda ake tuhumar ya yi lalata da cin zarafin yarinyar ne ta hanyar tsoma yatsansa a cikin al’auranta, wanda azaba tasa tayi ƙorafin jin zafi, kuma ta kai rahoto ga mahaifinta cewa wanda ake kayama aiki ne yai mata hakan fiye da sau ɗaya.
“An kai ta asibitoci uku, daga nan ne aka kama wanda ake zargin aka kai shi ofishin ‘yan sanda na Ojo.”
[…] Source link […]
[…] KU KUMA KARANTA:Kotu ta yankema mai koyan aiki hukuncin ɗaurin rai da rai, kan laifin yima jaririyar ubangidansa fy… […]