Kotu ta yanke wa ɓarawon turare hukuncin sharar kotu a Abuja

0
484

Wata kotu a Abuja ta yanke wa wani matashi da aka samu da laifin satar turare hukuncin sharar kotu.

Alƙalin kotun mai shari’a Ishaq Hassan ya umarci matashi mai shekaru 24 mai suna Valentine Nmoye da ya share harabar kotun da ke Karu a birnin tarayya Abuja na tsawon sa’o’i uku bisa samunsa da laifin satar turare guda uku na Naira 4,000 a wani shago.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito, Hassan ya bayar da umarnin ne bayan Nmoye ya amsa laifin sata. Alƙalin, ya kuma gargade shi da ya kiyaye aikata laifuka.

Tun da farko lauyan mai shigar da ƙara, Olanrewaju Osho, ya shaida wa kotun cewa wanda ya shigar da ƙarar, Sadiq Ahmed na kantin Tahalid Store da ke Garki a Abuja, ya kai rahoton faruwar lamarin a ofishin ‘yan sandan Garki a ranar 3 ga watan Nuwamba.

Da yake bayyana yadda Nmoye ya aikata laifin, Osho ya ƙara da cewa mai shigar da ƙarar ya ce wanda ake tuhumar ya shiga shagon ne ya sace turare guda uku, wanda kuɗinsu ya kai N4,000.

Osho ya kuma lura da cewa yayin binciken ‘yan sanda, wanda aka yanke wa hukuncin ya amsa laifin aikata laifin. Ya ce laifin da aka aikata ana hukunta shi ne a ƙarƙashin sashe na 287 na dokar Penal Code ta ƙasa.

Leave a Reply