Kotu ta umarci Yahaya Bello da ya miƙa kansa
Daga Ali Sanni Larabawa
Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta umarci tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello cewa ya miƙa wuya, ya bayyana a gaban ta domin ya fuskanci tuhumar zargin wawurar Naira biliyan 80 da ake masa.
Kotun wadda ta bayyana wannan umarni a ranar Talata, ta ce ya zama wajibi Yahaya Bello ya miƙa kansa ga Babbar Kotun Tarayya ta Abuja.
Alƙalai uku ne suka yanke wannan hukuncin a ranar Talata, a Kotun Ɗaukaka Ƙara, bisa jagorancin Mai Shari’a Hamma Barka, inda suka yi fatali da ƙarar da lauyan Yahaya Bello ya shigar a madadin sa, inda ya roƙi Kotun Ɗaukaka Ƙara cewa ta haramta wa EFCC kama shi da gurfanar da shi.
“Yahaya Bello ya gaggauta bin umarnin da Sashe na 396(2) na Dokar ACJA, domin ya gaggauta kai kan sa Babbar Kotun Tarayya, domin ya fuskanci tuhumar zargin karkatar da Naira biliyan 80 da EFCC ke yi masa.
KU KUMA KARANTA: EFCC ta ayyana neman Yahaya Bello ruwa a jallo
Mai Shari’a Kenneth Amadi ne ya karanta wannan hukuncin a madadin sauran alƙalan.
EFCC ta gurfanar da Yahaya Bello bisa zargin sa da kuma tuhume-tuhume guda 19, waɗanda suka shafi karkatar da Naira biliyan 80, a lokacin da yake gwamnan jihar ta Kogi.
Sai dai kuma bai yarda EFCC ta gabatar da shi cikin kotun ba, domin ya tsere, kuma tun lokacin ba a ji ɗuriyarsa ba.
An dai yi zama ɗai-ɗai har sau shida, ba tare da bayyanar Yahaya Bello ba, tun daga ranar 18 ga Afrilu zuwa ranar Talata da ta gabata.