Babbar Kotun Jihar Kano ta ba da umarnin a duba kwakwalwar Hafsat Suraj Chuchu wadda ake zargin ta da kisan wani mutum, mai suna Nafiu Hafiz.
Kotun ta ba da umarnin ne bayan Hafsat Chuchu ta ki yin magana bayan an karanta mata takardar zargin ta da kisan Nafiu Hafiz, wanda aka ce yaron gidanta ne.
Hafsat ta yi gum da bakinta ne bayan an karanta mata takardar ƙarar har sau biyar, a ci gaba zaman Babbar Kotun Jihar Kano a ranar Alhamis.
Wadda ake zargin ta ƙi furta ko kalma guda a kan ta aikata ko ba ta aikata ba da mai gabatar da ƙara ta ce ya saba da sashe na 221 na Pinal Kod.
Bayan haka ne mai gabatar da ƙara, Barista Aisha Mahmud ta nemi kotu ta yi umarni da a kai wacce ake zargin asibiti don gwada ƙwaƙwalwarta, dogaro da sashe na 286 na Kundin Laifuffuka na Jihar Kano na shekarar 2019.
Alkalin kotun Mai sharia Zuwaira Yusuf ta bayar da umarnin ɗaukar wacce ake zargin zuwa Asibitin Gwamnati don gwada ƙwaƙwalwarta.
KU KUMA KARANTA: Abokinsa da matarsa su suka shirya komai – Sanusi Ɗahiru Gwarando
Haka kuma su ma waɗanda ake zargin na biyu da na uku da na hudu an gurfanar da su gaban kotun inda aka zarge su da laifin boye gaskiyar bayanin rasuwar Nafiu Hafiz da niyyar kare wacce ake zargi.
Sai dai dukkaninsu sun musanta aikata laifin da ake zargin su da shi wanda ya saba da sashe na 167 na Kundin Pinal Kod.
Lauyoyin kariya Barista Haruna Magashi da Rabiu Abdullahi sun nemi kotu da ta bayar da belin su kuma a ta umarci masu gabatar da ƙara su ba su dukkanin takardun binciken shariar ciki har da rahoton ’yan sanda.
Sai dai masu gabatar da ƙara sun yi suka game da rokon nemen belin, inda suka buƙaci kotun da ta sa musu rana don gabatar da shaidunsu.
Alkalin Kotun Mai Shari’a Zuwaira Yusuf ta bayyana cewa kotun za ta sanar da ranar da za ta yanke hukunci game da rokon beli.
Idan za a iya tunawa ana zargin a ranar 21 ga Disamba 2023 wacce ake zargi, Hafsat Suraj, ta caka wa wani yaron gidanta mai suna Nafiu Hafiz wuka ta kashe shi.
Haka kuma su ma Dayyabu Abdullahi mijin Hafsat da Adamu Muhammad da Nasidi Muhammad su kuma ana zargin su da ɓoye gaskiyar musabbabin rasuwar Nafiu Hafiz.









