Kotu ta kori ƙarar da ke neman tsige babban sufeton ‘yan sandan Najeriya

1
398

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar talata ta yi watsi da ƙarar da ke neman tilasta wa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya tsige Sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba, bayan ya yi ritaya daga aiki.

Mai shari’a J.K. Omotosho ya ce wanda ya shigar da ƙarar, Michael Sam Idoko, ba shi da hurumin da zai iya kawo ƙarar. Alƙalin ya ce cikar wa’adin IGP da shekaru ba zai iya hana shi aikinsa na shekaru huɗu kamar yadda dokar ‘yan sanda ta 2020 ke ƙunshe da haka ba.

KU KUMA KARANTA: Hukumar ‘Yan sandan Najeriya ta kori jami’in ta dayayi zalunci

Idoko ya shigar da ƙarar yana mai cewa IGP Baba zai yi ritaya ne bayan ya kai shekaru 35 na aiki ko kuma ya kai shekara 60 da haihuwa.

A ƙarar da ya shigar da rundunar ‘yan sandan Najeriya da Usman Alkali Baba da majalisar ‘yan sandan Najeriya da shugaban kasa Muhammadu Buhari da babban lauyan gwamnatin tarayya, Idoko, ya ce ƙarin wa’adin da shugaban ƙasar ya yi wa IGP ya saɓa wa sashe na 215 (a) na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999.

1 COMMENT

Leave a Reply