Kotu ta ba da belin Dakta Idris Dutsen Tanshi bisa sharaɗi

1
352

Kotun Majistire a Bauchi ta bayar da belin malamin Musuluncin nan na jihar, Sheikh Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi.

A ranar Talata ne kotun majistire ta 1 ta yanke hukunci a kan buƙatar beli da lauyoyin fitaccen malamin mai janyo ka-ce-na-ce, suka nema bayan an gurfanar da shi a gaban kotu.

A ranar Litinin ne, ‘yan sanda suka shigar da Sheikh Idris Dutsen Tanshi gaban babbar kotun majistire ta ɗaya, inda suka tuhume shi da tada hankulan jama’a a karatunsa, inda ya yi kalaman rashin ɗa’a ga Annabi Muhammad (SAW). Sai dai malamin ya musanta zargin.

Lauyoyinsa sun shaida wa kotu cewa laifin da ake zargin malamin da aikatawa ba zai hana a bayar da shi belinsa ba, bisa tanadin dokokin Najeriya.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta tura Shaikh Abdul’aziz Dutsen Tanshi gidan gyaran hali a Bauchi

Daga nan sai alƙalin kotu ya sanya Talata a matsayin ranar da zai yanke hukunci game da buƙatarsu. Sannan ya ba da umarnin a ci gaba da tsare malamin a gidan yari kafin zaman kotu na gaba a washe gari.

Wata ƙungiyar addini mai suna Fityanul Islam ce ta kai ƙorafi kan malamin, tana zargin sa da furta miyagun kalamai a kan Annabi Muhammadu (SAW), sai dai Sheikh Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi da magoya bayansa sun ce zargin ba gaskiya ba ne.

Waɗanne ne sharuɗɗan beli?
Barista Alƙassim Muhammad, ɗaya daga cikin lauyoyin Sheikh Idris Abdul’aziz ya shaida wa BBC cewa kotun ta bayar da belin malamin ne bisa wasu sharuɗɗa.

Lauyan ya ambato kotu na cewa har yanzu dokokin Najeriya suna kallon malamin a matsayin wanda bai aikata wani laifi ba, don haka ba za a kama shi da laifi ba, har sai lokacin da aka tabbatar da da’awar da ake yi a kansa.

Ya ce sharaɗi na farko sai malamin ya gabatar da wani babban ma’aikacin gwamnati da ya kai matakin babban sakatare da kuma mai unguwa ko hakimi don su tsaya masa.

“Akwai kuma sharaɗin da za su gabatar da takarda, mallakan wani abu ko fili ko gida da ya kai naira miliyan biyar,” in ji Barista Alƙassim.

A cewarsa, kotu ta kuma buƙaci sai mutanen da za su tsaya wa Sheikh Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi, su gabatar da hotunansu ga rijistaran kotu, kafin sakin malamin.

Tun da farko, rahotanni sun ce magoya bayan malamin sun cika harabar kotun ta Mai shari’a Abdulfatah Shekoni duk da ɗimbim jami’an tsaro da aka jibge waɗanda suka riƙa taƙaita shige da ficen cincirindon mutane.

Sai an cika dukkan sharuɗɗan belin ne kafin a saki Sheikh Idris Abdul’aziz.

Za a ci gaba da sauraron ƙarar. Mai shari’a Abdulfatah Shekoni dai ya sanya ranar Laraba 24 ga watan Mayu, don ci gaba da zaman sauraron shari’ar ta Sheikh Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi da kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi.

Shari’ar dai ta ja hankalin ɗimbim mutane a ciki da wajen jihar.

A farkon watan Afrilu ne fitaccen malamin na jihar Bauchi ya furta wasu kalamai da suka tayar da ƙura a tsakanin takwarorinsa malamai da mabiyansu.

Yanzu dai za a zuba ido a gani shaidun da ɓangarorin biyu za su gabatar a wannan ƙara, kafin kotu ta kai ga yanke hukunci.

1 COMMENT

Leave a Reply