Kotu ta tura Shaikh Abdul’aziz Dutsen Tanshi gidan gyaran hali a Bauchi

2
972

Wata kotun Majistire a Bauchi ta ba da umarnin tsare wani malamin addinin Muslunci a jihar, Shaikh Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi a gidan yari, bisa kalaman tunzura jama’a karatunsa.

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ce ta gurfanar da malamin mai janyo taƙaddama a gaban kotu ranar Litinin, bayan ta gayyace shi game da wani ƙorafi da aka shigar gabanta.

A ranar 8 ga watan Afrilu ne, Hukumar Shari’ar Musulunci ta jihar Bauchi ta yi ƙarin haske a kan matakinta na ɗage wani zaman tattaunawa da ta shirya da Shaikh Idris Abdul’aziz, wanda aka yi zargin ya furta wasu miyagun kalamai a kan Annabi Muhammadu (SAW).

KU KUMA KARANTA: Zamfara: NUJ Ta Buƙaci Malaman Addini Da Kiyaye Furucinsu Lokacin Ramadan

Ana zargin fitaccen malamin ne da furta kalamin cewa ‘ba ya buƙatar taimakon Annabi’, abin da mafi yawan mutane ke ganin, munana lafazi ne kuma bai nuna biyayya ga Fiyayyen Halitta ba Annabi Muhammad (SAW).

Lamarin ya janyo muhawara mai zafi da ka-ce-na-ce har a tsakanin malaman addinin Musulunci da ke arewacin Najeriya, inda wasu suka fara kiraye-kirayen lallai hukumomi su ɗauki mataki.

Lauyan malamin Barista, Umar Hassan ya tabbatar da cewa an tsare malamin, bayan sun nemi a bayar da belin sa, inda kotu ta sanya Talata a matsayin ranar da za ta ba da hukunci a kan wannan buƙata.

Lauyan malamin ya ce ƙungiyar Fityanul Islam ce ta shigar da ƙorafi a gaban ‘yan sanda, abin da ya sa suka gayyace shi zuwa ofishinsu.

Ya ce ƙungiyar ta zargi Shaikh Idris Abdul’aziz da munana ladabi ga Annabi Muhammadu (SAW), kuma suka buƙaci a ɗauki mataki a kansa.

Lauyan ya nanata wa manema labarai cewa malamin ya sha musanta wannan zargi da ake yi masa.

A cewarsa tun makon jiya ne ya kamata malamin ya amsa gayyata, amma sai ya aika musu da cewa wani uzuri ba zai ba shi damar zuwa a lokacin ba.

2 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here