Kotu ta aike da Ɗanbilki Kwamanda gidan gyaran hali a Kano

0
87

Babbar Kotun Majistare da ke Kano ta tsare fitaccen ɗan siyasar nan, Abdulmajid ƊanBilki Kwamanda kan kalaman ɓatanci da ya yi wa tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso.

Kotun dai ta tsare ɗan siyasar ne dangane da cin zarafin tsohon gwamnan na Kano, wanda a bayan nan ya ce dole ne a waiwayi batun raba Masarautar Kano da takwaransa, Abdullahi Umar Ganduje ya yi.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta bayar da umarnin kama Dakta Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi

Dangane da buƙatar neman beli ce kotun ta ɗage zaman sauraron shari’ar zuwa ranar Litinin, 29 ga watan Janairu, inda ta ba da ajiyarsa a gidan kaso.

Leave a Reply