Kotu ta ɗaure ‘yar Italiya saboda neman ƙwace gidan da ba nata ba a Legas

0
499

Kotun hukunta laifuka na musamman a Jihar Legas da ke kudancin Najeriya ta ɗaure wata ‘yar ƙasar Italiya shekara uku a gidan yari saboda kama ta da laifin iƙirarin mallakar gidan da ba nata ba.

Mai Shari’a Mojisola Dada ta yanke hukuncin ne bayan ta kama matar mai suna Floriana De Stefani da laifi ɗaya cikin tuhuma shida da hukumar yaƙi da rashawa ta EFCC ta gabatar a kanta, a cewar rahoton Channels TV.

Alƙaliyar ta ce matar ta gabatar da takardun boge wajen ikirarin mallakar gidan da take haya a cikinsa bayan mutuwar mijinta mai suna Luca Signorelli.

A ranar 30 ga watan Maris na 2019 ne EFCC ta gurfanar da ita a gaban kotun tare da wata ‘yar Najeriya, Stella Ogboru, tana tuhumar su da laifi biyar wanda daga baya aka mayar da su shida kuma aka cire sunan ‘yar Najeriyar.

An tuhume ta da amfani da takardun ƙarya, da satar kadara, laifukan da ta musanta waɗanda kuma suka sa aka shiga shari’ar.

Leave a Reply